Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta noma hekta 500,000 domin bunƙasawa, wadatarwa da sauƙaƙa kayan abinci a faɗin Najeriya.
Tinubu bayyana haka a cikin jawabin sa na murnar shiga sabuwar shekarar 2024, wanda ya yi a safiyar Litinin.
“Za mu noma hekta 500,000 a faɗin ƙasar nan domin samun masara, shinkafa, alkama, gero da sauran kayan abincin da zai wadaci ‘yan Najeriya,” inji Tinubu.
Cikin watan Nuwamba ne dai Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin noman alkama a Jihar Jigawa, shirin da manoma 250,000 za su ci gajiyar noman alkama a Jigawa.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta tallafa wa kama daga ƙananan manoma 150,000 zuwa 250,000 da tallafin kashi 50 bisa 100 na kayan noma, domin samun damar noma hekta 200,000 zuwa 250,000, a wani gagarimin Shirin Noman Alkama a tsarin noman rani a Jihar Jigawa.
Ana sa ran samun alkama mai yawan tan 1,250,000.
Ministan Harkokin Noma da Bunƙasa Kayan Abinci, Abubakar Kyari ne ya bayyana haka, tare da cewa an bijiro da shirin domin rage tsadar kayan abinci da kuma rage dogaro da shigo da kayan abinci daga wajen ƙasar nan.
Kyari ya ƙara da cewa wani dalilin ƙirƙiro shirin kuma shi ne domin a samar da wadataccen abinci a cikin ƙasa.
Da ya ke magana a Haɗeja, yayin ƙaddamar da Shirin Bunƙasa Noman Alkama Cikin Rani, ya ce za a tabbatar cewa tallafin kayan noman zai iya ga mutanen da za a raba saboda su.
“Noman rani ya na ba mu gagarimar dama ta cin moriyar wawakekiyar ƙasa da albarkatun da ke cikin ta, wajen bunƙasa noma domin samun wadataccen abinci.”
Ya ce bayan ga noman damina da jama’a ke yi, wata hanya ta samar da abinci mai tarin yawa, ita ce noman rani, wanda har tattalin arzikin ƙasa ya ke bunƙasawa.
Ya ce Shirin Bunƙasa Noman Alkama a Lokacin Rani ya na ƙarƙashin Shirin NAGS-AP, wanda Gwamnatin Tarayya za ta gudanar daga lamunin dala miliyan 134 da aka ciwo a Bankin Bunƙasa Ƙasashen Afrika, wato AfDB.
Kyari ya ce shirin na daga cikin muradun Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ganin ana ƙara samun yawaitar jajirtattun manoma waɗanda za su bada himma sosai wajen noman irin su alkama, shinkafa, masara da rogo a faɗin ƙasar nan.
Ministan ya ce a ƙarƙashin wannan shiri, za a bai wa noman dawa, waken soya a lokacin damina.
“Manoman ƙasar nan sun kasance su ne jari mafi tsadar da wannan ƙasa ke tutiya da su a ko da yaushe. Saboda su ne ke wadatar da su da abincin da mu ke ci a ƙasar nan.
Discussion about this post