Shekaru 10 bayan Boko Haram sun sace ɗalibai sama da 200 a garin Chibok da ke Jihar Barno, ‘yan ta’adda sun sake afka wa al’ummar garin inda suka kashe aƙalla mutum 12, suka saci kayan abinci a gidaje da kantina, sannan kuma suka wasashe magungunan da ake asibitin garin.
Wannan hari na baya-bayan nan, an kai shi a ranar murnar sabuwar shekara, a Chibok, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Chibok ɗin.
Mazauna garin sun tabbatar da cewa an ji wa mutane da dama raunuka a mummunan harin da Boko Haram suka kai. Sun kwashi kayan abinci da kayan masarufi a gidaje da dama, sannan kuma suka afka cikin asibitin garin, suka kwashe magunguna.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Barno, Nahun Daso ya tabbatar wa wakilin mu da afkuwar lamarin.
Ya ƙara da cewa rundunar haɗa-ka tsakanin ‘yan sanda da sauran ɓangarorin tsaro na can na bin sawun ‘yan ta’addar har sai sun dangana maɓuyar su.
“An kai wannan mummunan hari a ranar 1 ga Janairu, tsakanin ƙarfe 5 na yamma zuwa ƙarfe 7 na dare.”
Ya ce mutum 12 aka kashe a harin, “kuma sun saci kayan abinci da magunguna”
Wani mazaunin Chibok mai suna Baba Barka, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa su na so jami’an tsaro su ƙara ƙaimi sosai a yankin na su.
Discussion about this post