A ranar Alhamis ne shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana fargabarsa kan yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, kamar yadda kakakinsa, Ajuri Ngelale, ya rubuta a wata sanarwa.
“Dole ne mu magance wannan matsalar ta hanyar kafa karin makarantu, daukar malamai, da kuma samar da akalla abinci daya a rana ga yaran makaranta.
Najeriya na da kimanin yara miliyan 20 da ba su zuwa makaranta, kamar yadda UNESCO ta kiyasta a shekarar da ta gabata, duk da cewa gwamnatin Najeriyar ta ce adadin na iya raguwa. Indiya ce kadai ke da yara da ba sa zuwa makaranta fiye da Najeriya, a cewar hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya.
Adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya na kara ta’azzara sakamakon rashin tsaro da ke ci gaba da addabar al’umomi da dama a arewacin Najeriya, lamarin da ya fidda dubban jama’a daga gidajensu da kuma kai ga rufe makarantu.
Shawarar da shugaba Tinubu ya bada ya hada da samun goyon bayan gwamnatocin jihohi don samun nasara akan haka. Galibin makarantun firamare da sakandare na gwamnati mallakar gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi ne wadanda kuma ke da alhakin daukar ma’aikata da gudanar da irin wadannan makarantu.
Tinubu ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da su maida hankali wajen ba ilimi kyakkyawar kula da kasu a jihohin su domin kawo karshen wannan matsala.
Discussion about this post