Kungiyar kare hakkin yara a Bayelsa, DO Foundation, a ranar Alhamis, ta yi fatali da auren gargajiya da aka yi a ranar 26 ga watan Disamba tsakanin wata ‘yar amarya ‘yar shekara hudu da wani mutum mai shekaru 54 a unguwar Akeddei da ke karamar hukumar Sagbama ta jihar.
Gidauniyar DO a cikin wata sanarwa da ta fitar a Yenagoa, ta bayyana auren a matsayin wanda ya sabawa doka, laifi da sannan ya sabawa kundin tsarin mulki da kuma dokar kare hakkin yara.
Kungiyar ta kuma bukaci a kama duk wadanda aka samu da laifi tare da gurfanar da su gaban kuliya.
NAN ta jiyo cewa an daura auren ‘yar yarinyar da wannan mai shekara 54 a gaban iyayenta ne wanda su ne suka ba da ita da kan su.
Ita dai wannan yarinya da bakinta ta ce wannan tsoho shine mijinta kuma dole a daura mata aure da shi domin ta ga ni cewa a wata rayuwar shine dai mijinta.
A dalilin haka ta gargadi iyayenta lallai su aura mata wannan tsoho idan ba haka ba za ta kashe kanta kowa ma ya rasa.
Discussion about this post