‘Yan bindiga sun kai hari kan al’umomi 15 a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na jihar Filato a jajibirin Kirsimeti, inda suka kashe mutane 96 tare da lalata gidaje 221, kamar yadda ‘yan sanda suka tabbatar.
Maharan sun kuma lalata motoci takwas da babura 27, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Alfred Alabo, mataimakin jami’in ‘yan sandan ya bayyana a ranar Talata a Jos, babban birnin jihar.
“A ranar 24 ga watan Disamba da misalin karfe 10 na dare ‘yan bindiga sun kai hari a kauyuka 15 a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi a lokaci guda.
“Binciken da aka yi a tantance abin da ya faru a Bokkos ya nuna cewa an kai hari kauyuka 12; an kashe mutane fiye da 79 tare da kona gidaje 221.
“An kai hari kan al’ummomi uku a Barkin-Ladi inda aka kashe mutane 17.
Ya lissafa al’ummomin da aka kai hari a karamar hukumar Bokkos da suka hada da Ndun, Ngyong, Murfet, Makundary, Tamiso, Chiang, Tahore, Gawarba, Dares, Meyenga, Darwat da Butura Kampani.
Discussion about this post