Shugaban Kasa Bola Tinubu, Gwamnonin Arewa da kungiyar Kiristocin Najeriya sun yi Allah Wadai da kisan kiyashin da aka yi al’umman jihar Filato.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Talata, shugaba Tinubu ya umurci hukumomin tsaro da su gaggauta fantsama cikin yankin, tare da kamo masu laifi.
Haka kuma shima shugaban Kunyar Gwamnonin Arewa Yahaya Inuwa na Gombe, ya yi alhinin abinda ya faru yana mai yin kira ga al’ummomin Arewa da Najeriya baki daya da su zauna lafiya a tsakanin su.
” “Abin takaici ne jin labarin hasarar rayuka sama da 100 da kuma asarar dukiyoyi da aka yi a lokacin wadannan hare-haren, musamman a lokacin da mutane ke shirin bikin Kirsimeti.
Yadda ‘Yan bindiga suka kashe mutum sama da 100 a Filato
‘Yan bindiga sun kai hari kan al’umomi 15 a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na jihar Filato a jajibirin Kirsimeti, inda suka kashe mutane 96 tare da lalata gidaje 221, kamar yadda ‘yan sanda suka tabbatar.
Maharan sun kuma lalata motoci takwas da babura 27, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Alfred Alabo, mataimakin jami’in ‘yan sandan ya bayyana a ranar Talata a Jos, babban birnin jihar.
“A ranar 24 ga watan Disamba da misalin karfe 10 na dare ‘yan bindiga sun kai hari a kauyuka 15 a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi a lokaci guda.
“Binciken da aka yi a tantance abin da ya faru a Bokkos ya nuna cewa an kai hari kauyuka 12; an kashe mutane fiye da 79 tare da kona gidaje 221.
“An kai hari kan al’ummomi uku a Barkin-Ladi inda aka kashe mutane 17.
Ya lissafa al’ummomin da aka kai hari a karamar hukumar Bokkos da suka hada da Ndun, Ngyong, Murfet, Makundary, Tamiso, Chiang, Tahore, Gawarba, Dares, Meyenga, Darwat da Butura Kampani.
Discussion about this post