Ministan Harkokin Ilmi, Tahir Mamman, ya bayyana cewa daga yanzu jami’o’in Gwamnatin Tarayya, Manyan Kwalejojin Fasaha da Manyan Kwalejojin Ilmi na Gwamnatin Tarayya ba su buƙatar neman iznin ɗaukar malamai, domin cike gurabun da babu a makarantun su.
Farfesa Mamman ya yi wannan albishir ne a ranar Alhamis, lokacin da ya ke jawabi wurin Taron Wakilan Majalisar Harkokin Ilmi ta Ƙasa, a Legas, wanda Gwamnatin Jihar Legas ta ɗauki nauyi.
Wannan sabon albishir ya zo ne kwana ɗaya bayan da Mamman ya bayyana wa duniya cewa Gwamnatin Tarayya ta tsame jami’o’i da manyan makarantun gwamnatin tarayya daga cikin tsarin biyan albashi na ƙeƙe-da-ƙeƙe, wato IPPIS.
Ya ce Gwamantin Bola Ahmed Tinubu ta maida hankali sosai wajen inganta harkokin ilmi, ta hanyar daina yi wa jami’o’i da manyan makarantu katsalandan.
Ya ce daga yanzu ba sun jira har sai Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ya ba su iznin ɗaukar ma’aikata domin cike gurbi ba.
Dokar hana ɗaukar malamai da gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ta ƙaƙaba, ta shafi manyan makarantu sosai, ta kai malamai da dama na barin ƙasar nan su na samun aiki a ƙasashen waje.
Haka kuma tsarin IPPIS ya sa jami’o’i ba su iya ɗaukar malamai na wucin-gadi, domin cike gurabun da suke da ƙarancin malamai.
Discussion about this post