Ƙungiyar Ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), ta dakatar da Jamhuriyar Nijar daga mamba a ƙungiyar, har sai bayan Sojojin Mulkin Nijar sun maida mulki a hannun farar hula tukunna.
Dakatarwar na ƙunshi cikin wata sanarwar da ECOWAS ɗin ta yi, bayan tashi daga taron da Shugabannin Ƙasashen ECOWAS suka gudanar a ranar Lahadi, a Abuja.
“Har zuwa ranar 10 ga Disamba, 2023, Shugabannin Ƙasashen ECOWAS na mai matsayar cewa abin da ya faru a Jamhuriyar Nijar, yunƙurin juyin mulki ne, kuma Mohammed Bazoum shi ne riƙe da gwamnati, ba sojojin juyin mulkin Nijar ba.” Haka sanarwar ta bayyana.
“Amma daga ranar 10 ga Disamba, ECOWAS ta yarda cewa an yi wa Gwamnatin Bazoum juyin mulki na soja.
“Don haka daga ranar 10 ga Disamba, ECOWAS ta dakatar da Nijar daga ƙungiyar, har sai lokacin da ƙasar ta koma mulkin dimokraɗiyya,” haka sanarwar ta bayyana.
A ranar Lahadi ce dai ECOWAS ta nemi Nijar ta saki Bazoum, iyalan sa da maƙarraban tsohuwar gwamnatin sa, idan ta yi haka, sai a cire mata takunkumi.
Sai dai kuma gwamnatin mulkin sojan Nijar ƙarƙashin Janar Abdourahmane Tchiani, ta ce ba za ta saki Bazoum ba.
Dama kuma a ranar Litinin Kotun ECOWAS ta yi biris da roƙon da Nijar ta yi a janye mata takunkumi.
Kotun Sauraren Ƙorafe-ƙorafe ta Ƙungiyar Ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) da ke Abuja, ta kori ƙara da roƙon da Jamhuriyar Nijar ta shigar, inda ta nemi kotun ta tilasta ECOWAS ta janye takunkumin da ta ƙaƙaba wa Jamhuriyar Nijar.
An ƙaƙaba wa Nijar takunkumi ne bayan sojoji sun kifar da gwamnatin farar hula ta tsohon shugaban ƙasa Mohammed Bazoum a cikin watan Agusta.
Duk da kotun ta ce ta na da iznin sauraren ƙarar, to amma kuma ta ce ba za ta iya bada umarnin a janye wa Nijar takunkumi ba.
Shugaban kotun, Edward Asante, wanda ya jagoranci alƙalai uku wajen sauraren ƙarar da yanke hukunci, ya ce Sojojin Mulkin Nijar sun kasa shigar da ƙarin bayanan da kotun ta nema a buƙatun da suka bijiro a kotun.
An yi wannan hukunci a ranar Alhamis, a zaman da alƙalan uku suka yi a Kotun ECOWAS da ke Asokoro, Abuja.
Sauran alƙalan sun haɗa Gberi-be Ouattara da kuma Dupe Atoki, duk sun amince ta ƙin cire wa Nijar takunkumi.
A ranar 26 ga Yuli ce Sojojin Nijar a ƙarƙashin Abdourahmane Tchiani suka kifar da gwamnatin Bazoum.
Daga nan take Shugaban ECOWAS, Bola Tinubu na Najeriya ya jagoranci ƙaƙaba wa Nijar takunkumi.
Najeriya ta rufe iyakokin ta da Nijar, kuma ta katse wa Nijar wutar lantarki a baki ɗayan ƙasar.
Dama daga Nijeriya ake bai wa Nijar wuta.
Takunkumin dai ya janyo ƙarin raɗaɗin tsadar rayuwa a Nijar da kuma Arewacin Najeriya, musamman a jihohi bakwai da suka yi iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Cikin makon da ya gabata ne Sanatocin Arewa suka yi kira ga Shugaba Bola Tinubu ya maida wa Nijar wutar lantarkin da aka katse mata, domin takunkumin ya na shafar harkokin kasuwanci da tattalin arzikin Arewa.
Discussion about this post