Tsohon Ƙaramin Ministan Tsaro, Musiliu Obanikoro, ya bayyana wa Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, yadda aka yi wa wani ƙaramin jirgin sama lodin naira bilyan 1.2 zunzurutu, daga Legas, aka kai wa tsohon Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose, a lokacin da ya tsaya takarar gwamna a 2014.
Ana zargin an kai masa kuɗin ne a cikin watan Yuli, 2014, wata ɗaya kafin sake zaɓen sa gwamna a ƙarƙashin PDP.
Fayose ya sake tsayawa takara a 2014, bayan ya yi zango ɗaya tsakanin 2003 zuwa 2006.
A 2014 ya kayar da gwamnan lokacin, Kayode Fayemi.
Naira biliyan 1.2 da ake shari’a kan ta a kotu, ta na cikin tuhumar da ake wani tsohon hadimin Fayose, mai suna Abiodun Agbele, a ƙarƙashin kotun Mai Shari’a Nnamdi Dimgba.
Shi ma Fayose ya na fuskantar irin wannan tuhumar, amma shi a wata kotun daban a Babbar Kotun Tarayya ta Legas.
Cikin Agusta 2016 ne EFCC ta gurfanar da Agbele bisa tuhumar sa da shi da wasu kamfanoni uku kan zargin laifuka 11 da suka ƙunshi satar Naira biliyan 4.7, kuɗaɗen makamai, wanda ya karɓa daga hannun tsohon Mashawarcin Shugaban Ƙasa na Harkokin Tsaro, Sambo Dasuƙi.
Cikin waɗanda ake zargin har da tsohon Ƙaramin Ministan Tsaro, Musiliu Obanikoro.
An yi zargin cewa Agbele da wasu kamfanoni uku sun karkatar da Naira biliyan 1.2, suka yi kasa-mu-raba a tsakanin su.
A ranar Laraba, Obanikoro ya bayar da shaida, a matsayin mai shaidar da EFCC ta gabatar, inda ya shaida wa kotu cewa, “mun loda Naira biliyan 1.2 wadda aka yi jigila sawu biyu, daga Legas zuwa Ekiti a wani ƙaramin jirgi.
“An kwashi kuɗaɗen daga wani asusu a Diamond Bank. Saboda kuɗin sun yi nauyi, sai da jirgin ya yi sawu biyu.”
Obasanjo ya ce bai san kuɗaɗen ko na me ba ne, amma dai Sambo Dasuƙi ne ya ce masa ga inda za a kai kuɗaɗen, wurin Fayose.
Za a ci gaba da zaman kotun a ranar 27 ga Fabrairu, 2024.
Discussion about this post