Gwamna jihar Kaduna, Uba Sani ya yaba wa kotun daukaka kara da alkalan uku da suka yanke hukuncin cewa shine yayi nasara a zaben gwamnan Kaduna.
A sanarwar nuna farinciki wacce kakakin gwamnan Mohammed Shehu ya fitar ranar Juma’a, Uba Sani ya jinjina wa kotun sannan ya yi kira ga abokanan hamayyar sa da su hakura kananan su zo a yi tafiya tare don ci gaban jihar Kaduna.
” Wannan hukunci da kotun daukaka kara tayi a yau juma’a ya tabbatar wa mutanen Kaduna abinda suka zaba a zaben Maris.
” Ba za mu yi kasa a guiwa ba wajen ganin mun ci gab da rangada wa muatanen jihar ayyuka na ci gaba babu kakkautawa.
Hukuncin kotun Daukaka kara
Kotun Daukaka kara a Abuja ta tabbatar wa Sanata Uba Sani da kujerar gwamnan Kaduna a hukuncin ta ta yanke ranar Juma’a a Abuja.
duka alkalai uka da suka saurari karar sun amince da hukuncin kotun farko wacce ta kori, karar sai da ta ce inda kotun baya ta ce za a iya cewa zaben bai kammalu ba kuskure ne.
Alkalan sun hakan bai taso ba kwatakwata domin tun farko jam’iyyar PDP da dan takaranta Isah Ashiru sun taf ka kuskure.
Kuskuren kuwa kamar yadda alkalan suka fadi shine akwai wani fom da ake cikawa kafin wani lokaci na a lokacin da ake shigar da kara wanda PDP da dan takaranta ba su shigar da shi ba da wuri har kwanakin mika fom din ya cika.
Bisa wannan dalilai kuwa ya sa ita kanta shari’ar bata da mazauni ballantana har a saurareta bisa dokar zabe da na kasa.
A dalilin haka ya sa kotu ta yi watsi da karar ta ce uba Sani ne gwamnan Kaduna wanda mutanen Kaduna suka zaba.
Discussion about this post