Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa za gurfanar da waɗanda aka damƙe a lokutan zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni a kotu.
INEC ta ce waɗanda za ta gurfanar ɗin dai an kama su ne a lokutan zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni, a ranakun 25 ga Fabrairu da 18 ga Maris, 2023.
Waɗanda za a gurfanar ɗin dai, za a gabatar da su ne a kotuna tare da gudummawar Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA).
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar da Babban Sakataren Yaɗa INEC, Rotimi Oyekanmi ya bayyana.
Da ya ke wa NDR bayani, Oyekanmi ya ce a Jihar Ebonyi ce aka fi kama masu laifukan zaɓe fiye da kowace jiha.
Ya ce INEC tare da haɗin guiwar ‘yan sanda sun shirya shigar da ƙararraki 191 ga ɗaukacin waɗanda ake zargin a jihohi daban-daban.
Daga cikin su, za a yi shari’u 64 a Jihar Ebonyi, inda aka kama waɗanda ake zargi yar 216.
A Jihar Edo, an kama mutum 80, sai Jihar Anambra inda aka kama mutum 66.
Daga cikin laifukan zaɓen da ake zargin sun aikata, Oyekanmi ya ce akwai “haɗa baki a yi kisa, mallakar bindigogi da albarusai ba tare da lasisi ba, fizgen akwati, ƙwacen kayan zaɓe, tarwatsa kayan zaɓe da lalata su.”
Sauran da ya lissafa sun haɗa da “rashin ɗa’a da tayar da hatsaniya a rumfar zaɓe da kuma satar sakamakon zaɓe.”
Discussion about this post