Bulalar majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewa dalilin da ya sa majalisar dokoki na kasa ya yi gaggawar amincewa da kasafin kudi na naira tiriliyan 2.1 shine saboda shugaban Kasa Tinubu ya gaggauta aiwatar da wasu ayyuka da ke gabansa dake bukatar a tunkaresu cikin gaggawa.
Ndume, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa, ya ce matakin da majalisun biyu suka yi sun yi ne domin amfanin kasar.
Sanata Ndume ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin da yake ganawa da manema labarai a harabar majalisar dokokin kasar.
Ndume ya ce an yi gaggawar zartar da dokar ne saboda akwai bukatar gwamnatin tarayya na biyan ma’aikata albashi kamar yadda kungiyar kwadago da ita gwamnatin suka amince.
“Sannan bayan haka akwai bukatar Hukumar Zabe ta kammala shirin gudanar da zaben gwamnoni da za ayi a jihohin Imo, Kogi da Bayelsa.
“A dalilin cire tallafin da gwamnatin tarayya ta yi, ya sa kayan abinci da na masarufi yayi tashin gwauron zabi a kasar nan.
“Sannan kuma akwai naira 35,000 da gwamnati ta yanke za ta baiwa ma’aikatan gwamnatin tarayya na wata 6, wanda duk yana kunshe a cikin wannan kasafi ne.
Discussion about this post