Ministan Abuja Nysom Wike ya bayyana wasu dalilan da ya sa suka kicime tsakanin sa da gwamnan jihar Simi Fubura da ya kaiga har ana ta bam a majalisar jihar sannan ana tafka artabu tsakanin jami’an tsaro a jihar.
Wike Ya fani wa gungun jigajigan PDP da suka ziyarce shi cewa, Fubura na neman wuce gona ne da Iri, bayan ya ga irin arangamar da muka yi da ‘yan adawa a jihar Ribas kafin shi ya zama gwamnan jihar.
” Ba zai yiwu ace da kai aka rika kai ruwa rana da ‘yan adawa, wadanda suka lashi takonin baza ka zama gwamna ba, amma na yi ruwa na yi tsaki na danne kowa sai da ka dare wannan kujera amma yanzu sai ka kwaso su ka rika dora su a wasu kujerun siyasa a jihar. Hakan ba zai sabu ba.
Bayan haka Wike ya karyata raderadin da ake cewa wai kudi ya ke nema a gwamnan ya rika bashi, wato kamar wani kasho daga asusun jihar.
” Ni ba butulu bane, abinda kawai zan gaya masa shine duk abinda zai yi ya yi abinshi can, amma jam’iyyar mu kada ya ce zai dagula mana tsari. Wannan shine abinda nake so kowa ya sani.
Idan ba amanta ba jihar Legas ta dagule a cikin makon jiya inda aka rika kai ruwa rana tsakanin Minista Wike da gwamnan jihar wanda ya nada Simi Fubara kan wasu sauye-sauye da ya kawo.
Discussion about this post