Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya da ta bude iyakokin Najeriya da jamhuriyar Nijar da aka rufe bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.
Majalisar ta bukaci gwamnati ta bude iyakokin Maigatari, Mai’Adua, Kongwalam da Illela.
Sai dai ‘yan majalisar sun ki amincewa da neman bude kan iyakokin kasar a kudancin Najeriya.
Dan majalisa Aliyu Madaki ya ce wuraren da ke kan iyakokin “an san su da manyan kasuwanni da ake gudanar da harkokin kasuwanci na kasa da kasa tsakanin ‘yan Najeriya da mutanen Nijar da Mali da Chadi da Kamaru da sauran kasashe makwabta.”
Dan majalisar ya bayyana cewa jihar Kano ta sha fama da matsalar rufe iyakokin kasar domin bin ka’idojin kungiyar ECOWAS.
Majalisar ta kuma bukaci kwastam da su daina muzgunawa ‘yan kasuwa da ke gudanar da ayyukansu a kan iyakokin kasar.
majalisar ta amince da a bude iyakokin sai dai kuma a halin da ake ciki dai bin wannan kudiri na iya yin barazana ga takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakabawa mulkin soja a Jamhuriyar Nijar.
Discussion about this post