Wata matar aure Rashidat Quadir a ranar Laraba ta kai karar mijinta kotu dake Centre-Igboro a Ilorin jihar Kwara inda ta nemi kotu ta raba aurenta da mijinta na shekara 11 saboda rashin kauna da kiyaya da iyayensa ke mata.
Rashidat ta ce kiyayyar dake tsakanin ta da mijinta da ‘yan uwansa ya samo asali saboda rashin haihuwa da bata yi.
Ta ce tun da ta auri mijinta shekaru 11 kenan Allah bai basu haihuwa ba.
“Mijina kan sa ni na rantse da sunnan Allah da Kur’ani mai girma idan na fita na dawo domin yana zargin cewa a duk lokacin da na fita na je saduwa ne sa wani a waje.
“Abin ya kai ga mijina kan bincika kayan da na saka na fita da su domin tabbatar cewa ban yi zina ba da wani ba,
“Wata rana mahaifiyar mijina ta ce mun tattara in koma gida saboda bata lokaci na ne kawai nake yi zaman da nake yi a gidan.
Rashidat ta ce bayan ta gaji da kiyayyar da ake nuna mata a gidan mijinta ne ta yi yaji watanni uku da suka gabata.
Mijin Rashida ya roki kotu kada ta raba auren saboda har yanzu yana son matar sa.
Ya ce tabbatar cewa babu kiyayyar tsakanin matar sa, shi da ‘yan uwansa.
“Na fita na je wurin aiki na dawo na iske matata ta yi yaji.
Alkalin kotun Shehu Ajimobi ya ba mijin daman shiryawa da matarsa.
Ajimobi ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 6 ga Nuwanba.
Discussion about this post