Sanatan Adamawa ta Arewa da kotun daukaka kara ta kora a ranar Litinin, Elisha Abbo, ya mika takardar neman yafiya ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, bisa zarginsa da yin tasiri kan hukuncin da kotun ta yanke a kansa.
Abbo, a wani taron manema labarai a ranar Litinin, ƴan sa’o’i kadan bayan kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta soke nasarar da ya samu a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Faburairu, ya shaida wa manema labarai cewa shugaban majalisar dattawan ne ya yi masa bita-da-Kullinbda kotu ta tsige shi.
Ya kuma yi zargin cewa za a kori wasu Sanatoci hudu da suka hada da Orji Kalu (Abia ta Arewa) da ke adawa da shugabancin Sanata Akpabio daga majalisar dattawa ta hanyar yanke hukunci a kotu nan ba da dadewa ba.
Sai dai a lokacin da tsohon Sanatan na Adamawa ya bayyana a gidan Talabijin na Arise News a daren ranar Talata, ya bayyana cewa duk zarge-zargen da ya yi wa shugaban majalisar dattawan karya ne kuma bai samu isassun bayanai ba kafin ya yi magana da manema labarai kan lamarin.
Don haka ya nemi afuwar Akpabio tare da neman gafara.
Dole ne in faɗi wannan tare da tawali’u da alhakin cewa sanarwar manema labarai da muka gabatar jiya (Litinin) ta kasance da wuri kamar yadda bayanan da muke da su a hannunmu suka nuna yanzu.
“Mun gano abubuwa da yawa jiya da daddare. Na kuma tattauna da shugabana, babban dan uwana, abokin aiki kuma shugaban majalisar dattawa, Sanata Akpabio, kuma na gamsu da cewa ba shi da hannu a tsigeni da kotu ta yi ta daga majalisar,” Na roke shi ya yafe min.
Idan ba a manta ba Abbo ya zargi Akpabio da yi masa bita-da-Kulli da ya yi sanadiyyar cire shi daga majalisar dattawa.
Discussion about this post