Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nysom Wike ya bayyana cewa rikicin siyasar jihar Ribas na jam’iyyar PDP ne, kuma jam’iyyar na duba lamarin.
Ana zargin Minista Wike, wanda tsohon gwamnan Ribas ne da hannu a yunkurin tsige magajinsa, Siminalayi Fubara.
Mafi yawa daga cikin Ƴan majalisar dokokin jihar na biyayya ga Wike ne, wanda tare da shi suka haɗa kai a tabbatar Fubara ya zama gwamna a wancan lokacin.
A sanadiyyar kokarin tsige gwamna Fubara ya yi sanadin tashin bam a wani bangare na harabar majalisar dokokin jihar Ribas, sannan wasu jami’an ‘yan sanda sun harba barkonun tsohuwa ga tawagar gwamna a lokacin.
Bayan haka, shugaban kasa da kansa ya sa baki a lamarin kamar yadda gwamnan Bauchi ya zayyana a hira da yayi da manema labarai bayan ganawa da suka yi a fadar shugaban kasa.
Wike ya bayyana cewa rikicin Ribas rikici ce ta jam’iyyar PDP, kuma PDP za ta warware matsalarta.
” Wannan rikici ta jam’iyya ce, kuma jam’iyyar mu ta PDP za ta warware wannan matsala. Rikice ce ta cikin gida kawai.
Discussion about this post