“Na yi wani bincike mai zurfi tsakanin 2018 zuwa 2020 ‘ƙarkashin gwamnatin Buhari’ a kan wasu mutane da kamfanoni 50. Binciken a kan harƙallar kwangila fa kaɗai na yi shi. Sai na bankaɗo cewa Najeriya ta ɗibga asarar Naira tiriliyan 2.9 da aka sace ta hanyar kwangiloli.”
Sabon Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya tabbatar da cewa an karkatar da aƙalla Naira tiriliyan 2.9 da sunan kwangiloli cikin shekaru uku a ƙasar nan, daga 2018 zuwa 2020.
Olukoyede ya bayyana haka a ranar Laraba, yayin da ya bayyana a gaban ‘Yan Majalisar Dattawa, domin fuskantar tantancewa.
Bayan an kammala yi masa tambayoyi da bayar da amsa, Majalisar Dattawa ta tantance shi.
Olukoyede ya yi bayani mai ratsa jiki cike da takaicin yadda ake satar kuɗaɗen Najeriya a ƙarƙashin shugabanni da jagororin da aka ɗora wa haƙƙin ragamar riƙon al’umma ko hukumomi da ma’aikatun gwamnati.
“Na yi wani bincike mai zurfi tsakanin 2018 zuwa 2020 a kan wasu mutane da kamfanoni 50. Binciken a kan harƙallar kwangila fa kaɗai na yi shi. Sai na bankaɗo cewa Najeriya ta ɗibga asarar Naira tiriliyan 2.9 da aka sace ta hanyar kwangiloli.”
Ya ce waɗannan maƙudan kuɗaɗe da aka sace a waɗannan shekarun da ya yi bincike, sun isa a yi amfani da su wajen gina wa ƙasar nan ayyukan raya ƙasa da inganta al’umma.
“Da shugabannin EFCC na baya sun hana a karkatar da waɗannan maƙudan kuɗaɗe daga 2018 zuwa 2020, to da an ci moriyar su ta hanyar yi wa ƙasa da ‘yan ƙasa ayyukan raya karkara da na ci gaban ƙasa baki ɗaya.
“Da na yi lissafi na, sai na gano cewa waɗannan kuɗaɗe har Naira tiriliyan 2.9, za su isa a gina titi mai tsawon kilomita 1,000, kuma a gina manyan jami’o’i da manyan makarantun gaba da sakandare guda 200 a faɗin ƙasar nan. Kuma duk a cikin kuɗaɗen za a iya ɗaukar nauyin karatun yara 6,000 daga firamare har zuwa jami’a, za a iya kashe wa kowane yaro Naira miliyan 16.
“Duk a cikin kuɗin za a iya gina gidaje 20,000 kowane gida mai ɗaki uku a faɗin ƙasar nan.
“Kuma a cikin kuɗin duk za’a iya gina asibiti na gani na faɗa guda ɗaya, a kowace jiha, har da Abuja.
“To kun dai ji daga inda muka fito da kuma inda muke a yanzu. Batun inda za mu dosa kuwa na hannun Majalisar Dattawa a yanzu, sai abin da ta yanke a yau ɗin nan.”
Ya ce zai shigo da tsarin yadda manyan ƙasurguman ‘yan Najeriya za su daina kinkimar kuɗaɗe su na sayen kayan alatu, ba tare da an riƙa kula da hada-hadar kuɗaɗen su ba.
“Idan za mu zuba ido mu ƙyale ‘yan Najeriya na sayen kantama-kantaman gidaje, rantsatstsun motoci da sauran kayan alatu, ba tare da tsarin biyan kuɗi na ƙeƙe-da-ƙeƙe ba, to ko za a kafa hukuma 1,000 ta yaƙi da cin hanci da rashawa, ba za su iya magance komai ba.”
Discussion about this post