Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa da ke Abuja ta yi watsi da karar da Peter Obi na jam’iyyar Labour ya shigar na kalubalantar zaben shugaban kasa Bola Tinubu.
Haruna Tsammani, wanda ke jagorantar alkalan mai mutum biyar, ya yi watsi da karar a hukuncin da ya karanta na tsawon sa’o’i a yau Laraba.
Tsammani ya ce masu shigar da kara sun kasa tabbatar da zargin cewa Tinubu bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shugaban kasa na 25 ba.
Ya yanke hukuncin cewa ba da dala 460,000 da wata kotu a Amurka ta bayar kan Tinubu dangane da shari’ar fataucin miyagun kwayoyi a shekarar 1993, bai zama dalilin hana shi tsayawa takarar shugaban kasa.
Ya kuma kara da cewa, sun kasa tabbatar da cewa zaben an tafka maguɗi a wuraren da suke korafi a kai, sannan ba su iya nuna wa kotu kwararan hujjoji na cewa an yi aringizon kuri’u a wuraren wasu wurare ba, gaba daya dai zarge-zargen na su ba shi da tushe.
Ya kuma yanke hukuncin cewa hujjar lauyoyin jam’iyyar Labour na cewa bai kamata a ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben ba saboda ya samu kuri’u kasa da kashi 25 cikin 100 a babban birnin tarayya Abuja, a matsayin ‘Tarkace da neman magana kawai’.
Kotun ta ce a baya kotun kolin ta yanke hukuncin cewa a dauki FCT tamkar daya daga cikin jihohin tarayya saboda haka FCT ba ta zama shafaffiya da mai ba. Ita ma kamar sauran jihohin kasar nan taka. Mutanen ta da kuri’un daidai suke da na sauran jihohin ƙasar nan.
Discussion about this post