Dangane da masifar ‘yan bindiga da ke ƙara muni a Bauchi, Gombe da Taraba, Gwamnonin Arewa maso Gabas sun fito ƙarara sun bayyana cewa akwai hannun sarakunan gargajiyar cikin yankunan karkara su na ɗaure wa ‘yan bindiga gindi.
Sun ce su ke yin haɗin-baki da ‘yan bindiga ana kisa da garkuwa da mutane a yankunan su.
Hare-haren ‘yan bindiga na ci gaba da muni a Bauchi, Gombe da Taraba, inda aka kashe ɗaruruwa a watannin baya-bayan nan.
Gwamnonin sun yi wannan zargi ne a ƙarƙashin Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas, bayan kammala taron su a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Gwamna Babagana Zulum na Jihar Barno ne ya karanta wa manema labarai takardar bayan taron wanda su ka kammala a ranar Asabar.
Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Gwamnan Adamawa, na Bauchi da na Yobe da Barno. Su kuwa Gwamnonin Gombe da Taraba duk mataimakan su ne su ka wakilce su.
Cikin takardar bayan taron wadda Zulum ya sa wa hannu a madadin sauran gwamnonin, su yi alƙawarin ɗaukar mataki da hukunci mai tsanani ga duk wani basaraken gargajiyar da aka samu da laifin goyon baya, ɗaurin gindi ko haɗa baki da ‘yan bindiga.
“Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas na sane da cewa wasu masu riƙe da sarautun gargajiya da shugabannin yankunan karkara na haɗa baki da ‘yan bindiga, su na ba su mafaka da maɓuya su na ta’addanci a yankunan Arewa maso Gabas.
“A kan haka mun yadda cewa za mu ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki a kan duk wani basaraken gargajiya ko shugaba a yankunan karkara, wanda aka kama ya na bai wa ‘yan bindiga mafaka, ko ya na haɗa baki da su.”
Gwamnonin sun ce sun lura yawan ragargazar ‘yan bindiga da sojoji ke yi a Arewa maso Yamma da sauran yankuna ne ya sa ‘yan bindiga ɗin ke yin hijira su na yin kaka-gida a Bauchi, Gombe da Taraba.
“Yayin da mu ke murna da godiya dangane da nasarar da aka samu wajen daƙile Boko Haram a wannan yankin, yanzu kuma wani sabon salon hare-hare na masu garkuwa ya buwaye mu, wanda ya ƙara munana mana matsalar tsaron da ke addabar yankin mu. To saboda ƙoƙarin da sojoji ke ci gaba da yi su na tarwatsa waɗannan ‘yan bindiga, sai su ke yin hijira daga wasu sassan ƙasar nan zuwa nan Arewa maso Gabas.
“Lamarin na ƙara muni sosai a Bauchi, Gombe da Taraba, wuraren da a shekarun baya babu matsalar ‘yan bindiga.”
Gwamnonin sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya ya gaggauta shawo kan lamarin hare-haren na ‘yan bindiga.
Haka kuma sun ce yawaitar masu haƙar ma’adinai barkatai na ƙara rura wutar ‘yan bindiga. Sai su ka dangana da cewa akwai alaƙa tsakanin haƙar ma’adinai da kuma hare-haren ‘yan bindiga.
Sun nuna damuwa kan yawaitar masu haƙar ma’adinai ba tare da lasisin izni ba.
Discussion about this post