Hedikwatar tsaron Kasa DHQ ta bayyana adadin yawan sojojin da suka mutu a harin da aka yi a jihar Neja ranar Litini.
Shugaban yada labarai na Hedikwatar Tsaron Edward Buba da yake ganawa da manema labarai ya ce sojoji 36 ne suka rasa rayukansu a harin.
Buba ya ce a harin da aka yi a Zungeru manyan sojoji uku da sojoji 22 ne suka mutu sannan wasu guda bakwai sun ji rauni.
Bayan haka ne aka aika jirgin sama ya dauko gawarwakin su da wadanda suka ji rauni, amma kuma a hanyarsa ta dawowa sai ya yi hatsari ya fado kasa a kauyen Chukuba dake karamar hukumar Shiroro
A lokacin jirgin ya kwashi gawan sojoji 14, sojoji 7 da suka ji rauni sannan akwai matuka jirgin su biyu da sauran ma’aikata a cikin jirgin.
Edward Gabkwet ya ce har yanzu ba a gano dalilin da ya sa ya fado ba, sannan yayi gargadi ga mutane su daina yada jita-jita domin kauce wa tada zaune tsaye.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin iƙirarin su Gogarma Dogo Giɗe, inda ya ce ”Mu muka harbo jirgin sojojin da ya faɗo a yankin Shiroro”
Gogarman ɗan bindigar nan mai alaƙa da Boko Haram ɓangaren Ansaru, wato Dogo Giɗe, ya bayyana cewa su ne su ka harbo jirgin Sojojin Saman Najeriya, wanda ya faɗi yayin da ya ke ɗauke da sojojin da suka jikkata a wani gumurzu a jihar Neja.
Jirgin wanda ya faɗi ranar Litinin, ya tashi ne ɗauke da wasu sojoji da nufin zai garzaya da su Asibitin Sojoji na Kaduna.
A cikin wani bidiyo na minti 2 da sakan 17, wanda PREMIUM TIMES ta kalla, kuma wata majiyar jami’an tsaro ta tabbatar da sahihancin bidiyon, an nuno dakarun Dogo Giɗe su na murnar sun harbo jirgin samfurin helikwafta a ƙasa. An riƙa jin wata murya mai bayyana yadda aka harbo jirgin.
“Ga gawarwakin sojojin da suka mutu a wurin hatsarin muna nuna maku. Gawarwakin sojojin da su ka kawo mana hari nan, da niyyar karkashe mu.” Haka wani mai muryar Fulani ya bayyana a cikin harshen Hausa, yayin da ya ke nuna helikwaftan.
“Sun so su kashe Dogo Giɗe. Amma Dogo Giɗe da yardar Allah ya na raye, kuma sojoji ba za su iya kashe shi ba.
“Ina so ku jama’a ku tuba, domin na mu da matsala da kowa. Ba za mu kashe kowa ba, sai wanda ya shirya kai mana hari.
“Ku dubi wannan nasara, Allah ne ya ba mu karfin kakkaɓo jirgin.”
Ya ce ya na so shugabannin da ke aiko sojoji don su kashe su, cewa su tuba, domin su Dogo Giɗe ba su son a zubar jini.
An riƙa jin sautin kabbara daga gefe, ana kuma dariyar-ƙeta.
Discussion about this post