Yayin da a Burkina Faso ta kulle gidan radiyon da ya watsa tattaunawa da masu adawa da juyin mulkin Nijar, a Jamhuriyar Benin kuwa gidan talabijin, radiyo da jarida aka kulle, saboda rahotonnin da ke da nasaba da rashin goyon bayan ECOWAS, Bazoum da takunkumin da aka garƙama wa Nijar.
Hukumar Harkokin Sadarwa ta Jamhuriyar Benin (HAAC), kulle gidajen Talabijin, Radiyo da Jarida na Gazette du Golfe, bayan ta zargi kafafen yaɗa labaran da ƙin bin ƙa’idojin da hukuma ta bayar wajen bada labaran da suka shafi juyin mulki a Afrika da Afrika ta Yamma.
Wani jami’in HAAC ya shaida wa CPJ cewa an kulle kafafen watsa labarai na Gazette du Golfe a ranar 8 Ga Agusta, saboda sun soki shirin yin amfani da ƙarfin soja don a hamɓaras da sojojin mulki a Nijar.
Jamhuriyar Benin dai ta na cikin ƙasashen da suka amince su tura sojoji a Nijar, a ƙarƙashin rundunar ECOWAS, domin a maida hamɓararren Shugaban Ƙasa, Mohammed Bazoum kan mulkin sa.
A Burkina Faso kuwa, Hukumar Yaɗa Labarai ta dakatar da Radio Omega, sanadiyyar wata tattaunawa da ya yi da wani mai suna Ousmane Abdoul Moumouni, Kakakin Majalisar Tawaye ga Gwamnatin Sojoji, wadda aka kafa domin a maida Bazoum kan mulkin sa.
Sanarwar da aka bayar ta dakatar da Omega Radio, ta ce “tattaunawar da aka yi da Moumouni cike ya ke ga ɓatanci da cin zarafin mahukuntan Nijar.”
Ita dai Burkina Faso ta ce za ta yi yaƙi da duk ƙasar da ta kai wa Nijar farmaki.
Radio Omega ya ce jami’an ‘yan sanda sun gayyaci babban editan radiyon, Abdoul Fhatave Tiemtore, a ranar 11 Ga Agusta, su ka tsare shi wasu sa’o’i, daga baya suka sake shi bayan sun yi masa tambayoyi.
Radio Omega ya yi tir da wannan dakatarwar, tare da cewa hukuma ta yi haka ne kawai saboda wasu masu goyon bayan juyin mulkin Nijar sun yi masa barazana, tare da kiran cewa a dakatar da wanda ya watsa tattaunawar.
Discussion about this post