Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Janar Taoreed Lagbaja, ya ƙara yin kira ga Sojojin Najeriya cewa su kasance su ci gaba da jajircewa wajen ƙoƙarin kakkaɓe duk wasu abokan gabar Najeriya, domin su kawo zaman lafiya a faɗin ƙasar nan.
Lagbaja ya yi wannan kira a ranar Laraba, yayin da ya kai masu ziyara a Jihar Neja, domin duba irin ɓarnar da ‘yan ta’adda su ka yi masu a wani sunƙuru da su ka yi wa sojojin a Zungeru.
An dai yi asarar rayukan wasu sojoji a gumurzun na su da ‘yan ta’addar.
Wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Rundunar Sojojin Najeriya, Onyema Nwachukwu ya fitar a ranar Laraba, ta ce Lagbaja ya isa Minna, babban birnin Jihar Neja a cikin dare, ranar Talata.
Burgediya Janar Nwachukwu ya ƙara da cewa daga nan ba tare da ɓata lokaci ba, Lagbaja ya zarce Sansanin Operation Base Erena da ke cikin Ƙaramar Hukumar Shiroro, inda aka sanar da shi irin matsalar tsaron da ke yankin.
GOC na Bataliya ta 1, Manjo Janar Bamidele Alabi ne ya yi masa cikakken bayani.
Yayin da ya ke wa dakarun jawabi, Lagbaja ya ƙara yin kira gare su cewa su ci gaba da haɗa kai wajen ƙara ƙwazon kakkaɓe maƙiya Najeriya.
Ya ce yaƙi da ta’addanci da ‘yan bindiga tsananin kishi ne ga Najeriya, domin kare ta da kuma kare ‘yan Najeriya baki ɗaya.
Ya ce aiki mafi tsada ga ƙasa shi ne aikin kare rayukan jama’a da kuma kare ƙasa.
Daga nan ya ƙara yi masu tabbacin ƙara ƙaimi wajen kula da haƙƙoƙin su da jin daɗi da walwalar iyalan su.
Daga nan ya bada umarnin a ƙara yawan sojoji a rundunar da kuma ƙarin kayan fama.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin iƙirarin su Gogarma Dogo Giɗe, inda ya ce ”Mu muka harbo jirgin sojojin da ya faɗo a yankin Shiroro”
Gogarman ɗan bindigar nan mai alaƙa da Boko Haram ɓangaren Ansaru, wato Dogo Giɗe, ya bayyana cewa su ne su ka harbo jirgin Sojojin Saman Najeriya, wanda ya faɗi yayin da ya ke ɗauke da sojojin da suka jikkata a wani gumurzu a jihar Neja.
Jirgin wanda ya faɗi ranar Litinin, ya tashi ne ɗauke da wasu sojoji da nufin zai garzaya da su Asibitin Sojoji na Kaduna.
A cikin wani bidiyo na minti 2 da sakan 17, wanda PREMIUM TIMES ta kalla, kuma wata majiyar jami’an tsaro ta tabbatar da sahihancin bidiyon, an nuno dakarun Dogo Giɗe su na murnar sun harbo jirgin samfurin helikwafta a ƙasa. An riƙa jin wata murya mai bayyana yadda aka harbo jirgin.
“Ga gawarwakin sojojin da suka mutu a wurin hatsarin muna nuna maku. Gawarwakin sojojin da su ka kawo mana hari nan, da niyyar karkashe mu.” Haka wani mai muryar Fulani ya bayyana a cikin harshen Hausa, yayin da ya ke nuna helikwaftan.
“Sun so su kashe Dogo Giɗe. Amma Dogo Giɗe da yardar Allah ya na raye, kuma sojoji ba za su iya kashe shi ba.
“Ina so ku jama’a ku tuba, domin na mu da matsala da kowa. Ba za mu kashe kowa ba, sai wanda ya shirya kai mana hari.
“Ku dubi wannan nasara, Allah ne ya ba mu karfin kakkaɓo jirgin.”
Ya ce ya na so shugabannin da ke aiko sojoji don su kashe su, cewa su tuba, domin su Dogo Giɗe ba su son a zubar jini.
An riƙa jin sautin kabbara daga gefe, ana kuma dariyar-ƙeta.
Wane Ne Gogarma Dogo Giɗe?:
Shi ne ɗan bindigar da ya kashe gogarma Tsoho Buhari cikin 2018.
Giɗe ya kashe Buharin Daji yayin da suke wata gardama, bayan Buhari ya sato shanun surukin Dogo Giɗe.
Daga nan Giɗe ya ƙara zama hatsabibi, har ta kai ya ƙulla alaƙa mai ƙarfi da Boko Haram.
Giɗe haifaffen yankin Erana ne, cikin ƙaramar hukumar Shiroro ta Jihar Neja.
Giɗe ya haɗa zuga da Ali Kawajo, wato Kachalla, wanda shi ma a cikin 2022 ya taɓa harbo jirgin sojoji a Dajin Zamfara.
Kuma ya na da alaƙa sosai da Malam Abba, gogarman ‘yan Boko Haram ɓangaren Ansaru, waɗanda suka yi fashin jirgin ƙasa a kan hanyar sa daga Abuja zuwa Kaduna, cikin Maris, 2022.
Kuma shi ne ya kwashe ɗaliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Yauri.
Kakakin Yaɗa Labaran Sojojin Saman Najeriya, Edward Gabkwet bai ɗaga kiran wayar da wakilin mu ya yi masa, domin ya ji ta bakin sa ba.
Discussion about this post