An ƙididdige cewa yawan ɗalibai mata da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga su ka sace tun bayan sace ɗaliban Chibok su 276 cikin 2014, za su kai 1,680.
Kungiyar Kare Ɗalibai Mata da Ƙananan Yara, wato ‘Save The Children ce ta fito wa wannan rahoto a ranar 18 Ga Agusta, 2023.
STC ta ce ta ce ƙididdigar ta tsaya ne a ƙarshen Disamba, 2022, kenan ba ta lissafa da waɗanda aka sace a 2023 ba.
Yayin da har yanzu fiye da ɗaliban Chibok 90 ba a san halin da su ke ba, wannan adadin da STC ta lissafa bai bayyana yawan ɗaliban da har yanzu ke a hannun ‘yan bindiga ba, musamman waɗanda suka aure su da ƙarfin tsiya.
Rahoton STC ya ce a cikin waɗannan shekaru 10 ɗin, an kashe ɗalibai mata har 180, an jikkata wasu kusan 90 a hare-haren da aka kai makarantu 70.
“Yayin da aka kai hare-hare makarantu 49 a Arewa maso Yamma, an kai wa makarantu 11 hari a Arewa ta Tsakiya.
“Aƙalla an sace malamai 60, an kashe 14, an ragargaza makarantu 25.
“A jihar Katsina an rufe kusan makarantu 100 saboda matsalar tsaro, wadda ta shafi fiye da ɗalibai 30,000.
STC ta ce a binciken da ta yi, ɗalibai da dama mata sun bayyana cewa su na tsoron komawa makaranta.
Wata ɗaliba cewa ya yi, ta na jin tsoron komawa makaranta, don kada a sake yin garkuwa da ita, ko a yi mata fyaɗe.
Daraktan STC a Najeriya, Famari Barro, ya ce akwai buƙatar ƙara matakan tsaron ɗalibai mata da ƙananan yara.
Discussion about this post