Hukumar Jami’oi ta kasa ta baiwa Farfesa Adamu Gwarzo shaidar amincewa da fara karatu a Sabbin Jami’oin sa da ya kafa da suka hada da
1- Canadian University of Nigeria Abuja da
2- Franco British International-FBI University Kaduna.
Kafin kafa waɗannan jami’o’i biyu, farfesa Gwarzo ya kafa jami’ar Maryam Abacha, dake Kano da kuma wacce ta ke Maraɗi, Jamhuriyar Nijar.
Farfesa Gwarzo ne mutum na farko a yankin Arewa da ya kafa jami’o’i har guda uku a yankin Arewa da kuma yake baiwa yara da dama tallafin guraben karatu kyauta.
A jawabin godiya da yayi wa gwamnatin Najeriya a lokacin da aka bayyana sunayen jami’o’in a cikin jami’o’i 37 da gwamnati ta amince Farfesa Gwarzo ya ce ” Babban burina shine in ga ilimi ya wanzu a tsakanin al’ummar mu gaba ɗaya. Za mu ci gaba da yin haka da kuma tallafa wa ƴaƴan mu musamman marasa karfi domin samun guraben karatu a ire-iren wadannan jami’o’i manya, domin ci gaban al’umman mu da kasa baki ɗaya.
Discussion about this post