Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama mutum 57 da suke sace kayan mutane a shagunan da gwamnati ta rusa a jihar.
Kakakin rundunar Abdullahi Kiyawa wanda ya sanar da haka ya ce rundunar an kama wadannan mutane bisa laifin sata da shiga shagunan mutane ba tare da izini ba.
“Baya ga mutum 49 din da muka kama da farko rundunar ta kara kama wasu mutum 57 jimlan 106 da laifin satar kayan mutanen da gwamnati ta rusa.
“Mun kai wadannan mutane kotun majistare dake 35 Normans Land a Kano domin yanke musu hukunci.
“Rundunar ta yi kira ga duk wadanda aka yi wa sata da su zo ofishin ‘yan sanda dake Bompai domin karbar kayayyakin su da aka sace ko kuma su kira wannan lanbar kamar haka 08038249455.
Discussion about this post