Matasa sun kashe wani mahauci mai suna Usman Buda bayan an zarge shi da yin kalaman batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad a Sokoto ranar Lahadi.
Lamarin ya auku ne a hanyar abbatoir da misalin karfe 10:37 na dare.
Wani ganau wanda ya bayyana sunansa da Aliyu, ya shaida wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho cewa Buda ya yi kalaman batanci kuma ya maimaita sau uku a lokacin da wasu su tuhume shi kan zargin, sai ya rika maimaita abinda yace har sau uku.
“Akwai wani Dan uwana dake wannan wuri wato layin Abbatoir a lokacin da abin ya faru, lokacin da Usman (Mr Buda) ya zagi Manzon Allah, wasu sun ce yana da tabin hankali amma mafi yawan wadanda suke kusa da shi, wadanda abokan kasuwancinsa, sun ce ba a taba sanin cewa yana da matsalar tabin kwakwalwa ba.
Wasu matasa sun nemi ya janye wadannan kalamai na batanci da ya yi a kan Annabin SAW, sai ya ce sam ba zai janye ba. Daga nan ne suka fara surfar sa da duka ta ko’ina.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin. Sai dai ta ce ko da ta isa wurin da ake jibgar wannan mutum sun iske shi kwance rai a hannun Allah, sannan yaran dake kilar sa duk sun arce.
Kakakin rundunar ya ce tuni ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike akai domin sanin ainihin abinda ya faru da kuma kamo wadanda suka dauki hukunci a hannun su.
Discussion about this post