Wata matar aure mai suna Zulai Umar ta ruga babbar kotu a Gwagwalada Babbar Birnin Tarayya Abuja domin kotun ta raba auren ta na shekara 14 saboda kiyayyar juna da ya shiga tsakaninta da mijinta Abubakar Umar.
Zulai ta ce sun haifi ‘ya’ya biyar tare da Umar sannan suna zama a Giri Gauta dake Gwagwalada ne.
Ta ce ta fara samun matsaloli a auren ta ne tun a shekarar 2015 domin a lokacin ne Umar ya fara shan giya.
“Na roke Umar ya daina shan giya amma yaki Ji. A ranar 20 ga Yunin 2020 a taron sunan dan da na haifa na ƙarshe Umar ya shigo wurin taron a maske yana warin barasa, sannan ya rika yada abin kunya a gaban sirikan sa.
“A dalilin haka ya sa na yi fushi na koma gidan iyaye na da zama tare da ‘ya’yan mu duka.
Zulai ta ce ta yi wata 10 a gida iyayenta amma ko sau daya Umar bai taba zuwa ganin ta da ‘ya’yan su ba.
Ta ce ta gaji da zaman auren Umar saboda ta gano cewa baya son ta kuma baya son auren.
Abubakar ya shigo kotun a maske da giya inda hakan ya sa ya kasa yin magana mai ma’ana a kotun.
A dalilin haka alkalin kotun Abdullahi Abdulkarim bayan ya ja kunnen Umar ya daga shari’ar zuwa ranar 23 ga Yuni domin Umar ya zo ya amsa laifukan da matarsa ta ke zargin sa akai.
Discussion about this post