Wasu Kiristoci da dama a ranar Asabar sun fito sun hada hannu da Musulmai domin gyara filin Idi a karamar hukumar Kachia jihar Kaduna.
Jessica Akila da Mercy Bajumi mambobin kungiyoyi masu zaman kansu na ‘Community Peace Observers (CPO)’ da ‘Community Initiatives to Promote Peace (CIPP)’ sun ce sun yi haka ne domin inganta zaman lafiya dake tsakanin Kiristoci da Musulmai a jihar Kaduna da kasa baki daya.
Sun ce wannan shine karo na biyu da suke fitowa da yawan su domin gyara filin Idin dake karamar hukumar Kachia.
Sun yi bayanin cewa sun zo ne domin su taya musulmai cirbe ciyawan da suka fito.
Shima jami’in kungiyar CPO Daniel Bitrus ya ce sun fito ne domin inganta zaman lafiya tsakanin Kiristoci da Musulmai a yankin.
Kungiya mai zaman kanta na ‘Conflict Mitigation Management Regional Council (CMMRC)’ na daga cikin kungiyoyin da suka fito domin taya musulmai cirbe filin Idin.
Daga nan sakataren Jama’atu Nasril Islam (JNI) na karamar hukumar Kachia Ibrahim Tasiu ya yaba kokarin da matasa da dattawa suka yi wajen hada kan Kiristoci da Musulmai domin tsaftace filin idin.
Discussion about this post