Jami’an hukumar kwastam ta Najeriya a wani shingen bincike a karamar hukumar Garki ta jihar Jigawa a ranar Juma’a sun harbe wani abokin aikinsu da ke dawowa daga jamhuriyar Nijar, bayan ya ki tsaya a yi masa bincike.
Jami’an kwastam ɗin dake aiki a wannan shingen binciken sun afka cikin shakku a lokacin da motar jami’in mai suna Muhammad Sayyadi, ya nufo wannan shinge sannan ya ki tsayawa a bincike shi.
A cikin rashin sani, ashe Sayyadi jami’in hukumar ne da ke aiki hukumar a Legas.
Yana dawowa daga garin Magarya ne, bayan ta’aziyya da ya kai wa tsohon jakadan Najeriya a Korea Ta Kudu, Ali Magashi bisa rasuwar mahaifiyar sa.
Sai dai kuma lamarin ya nemi tada hankalin mutanen yankin Ringimna lokacin da suka fahimci cewa Sayyadi dan Sarkin Ringim ne.
Sai dai komai ya lafa bayan dan wani lokaci. Sayyadi yana Asibitin Aminu Kano a na duba shi.
Discussion about this post