Gwamnan Jihar Ribas mai barin gado, Nyesom Wike, ya roƙi zaɓaɓɓun ‘yan majalisa 13 na Ribas duk su zaɓi Tajuddeen Abbas domin zama Kakakin Majalisar Tarayya.
Wike ya ce zai yi kamfen wurjanjan, domin tabbatar da cewa ba a maimaita irin abin da ya faru wajen zaɓen Kakakin Majalisar Tarayya a 2015 ba.
Wike ya yi wannan roƙo a ranar Juma’a a Fatakwal, lokacin da Honorabul Abbas da ‘yan tawagar sa su ka kai masa ziyara a Fatakwal.
Wike ya ce shi da kan sa zai shiga cikin rundunar kamfen ɗin Abbas, bayan ya sauka daga mulki, domin tabbatar da cewa ɗan majalisar ya samu nasara a zaɓen shugabannin majalisa, wanda za a yi cikin watan Yuni.
Ya ce zai yi bakin ƙoƙarin sa domin ganin ba a maimaita irin zaɓen Kakakin da aka yi a 2015 ba.
A 2015 dai wasu ‘yan APC da kuma ‘yan adawa daga PDP, sun haɗe kai, su ka zaɓi shugabannin majalisa.
“Ina tabbatar maku cewa ina tare da ku. Lokacin da Kingsley Chinda ya shaida min ku na tafe, na ce masa ai babu amfanin har sai kun yi wahalar tattaki zuwa wuri na. Domin ina tare da ku. Dukkan mambobin Ribas na tare da ku, banda mutum ɗaya, wanda ke ta bankaurar sa shi kaɗai.
“Saboda haka ina roƙon mu ci gaba da goyon bayan Abbas. Kada kuma ku riƙa goyon bayan sa da rana, da dare kuma ku goyi bayan wani can daban.” Inji Wike.
Discussion about this post