Tun tashin farko dai Gwamna Matawalle rabo ne ya kai shi zama gwamna a Jihar Zamfara, amma ba yawan ƙuri’u ba.
A ƙarƙashin PDP ya yi takara a 2019. Bai ci zaɓe ba, saboda na biyu ya zo. Ya zama gwamna ne a ɓagas, saboda Kotun Ƙoli ta kori duk wani ɗan takara na Jihar Zamfara, tun daga gwamna, mataimakin gwamna, sanatoci da mambonin tarayya. Duk wadanda su ka yi wannan takara a ƙarƙashin APC, sai da Kotun Ƙoli ta kore shi.
Bayan ya zama gwamna, Matawalle daga baya ya koma PDP, sai dai hakan bai sa ya sake yin nasara a 2023 ba. Saboda Dauda Lawal ya yi masa sukan-kabarin-kishiya a zaɓen gwamna. Hakan ya sa PDP za ta koma kan mulkin jihar kenan daga ranar 29 Ga Mayu, 2023.
Daga cikin abubuwan da Matawalle ya yi alƙawarin magancewa a jihar, a lokacin kamfen ɗin 2019, akwai matsalar rashin aikin yi ga matasa, fatara da talauci da kuma farfaɗowa tare da inganta ilmin zamani.
Sai ga shi jadawalin tantagaryar talauci (multidimensional poverty index) na 2022, ya bayyana cewa kashi 78 na Zamfarawa kwana da tashi su ke yi a cikin matsalancin talauci da fatara mai zafin gaske.
Hakan ya na nufin maimakon a samu sauƙi a zamanin mulkin Matawalle, sai ma malejin fatara ɗin ne ya ƙara cillawa sama zuwa kashi 74 ko kashi 78 bisa 100 na dukkan al’ummar jihar.
Idan aka koma batun ciwo bashi kuwa, a 2019 ana bin jihar bashin Naira biliyan 103.35. Zuwa 2021 ya kai Naira biliyan 130.94.
Hakan ya nuna ita ce jiha ta biyu da aka bin ta bashi mai tarin yawa a jihohin Arewa maso Yamma. Kuma ta 15 a jerin jihohin da ake bi bashi a Najeriya.
Rashin Aiki Yi Ya Haɗu Da Fatara Da Matsalar Tsaro:
Yayin da Matawalle bai inganta komai ta finnin tallalin arzikin jihar sa ba. Gwamnatin ta ce ta samar wa mutum 6,000 aiki tsakanin 2019 zuwa 2022.
Ilmi Bai Samu Kulawa Daga Matawalle Ba:
Binciken da UNESCO ta fitar da rahoto cewa Gwamnatin Matawalle ba ta yi hoɓɓasa wajen inganta harkokin ilmi a Zamfara ba.
Binciken da UNESCO ta fitar cikin 2023, ya tabbatar da cewa kashi 61. 4 na ƙananan yaran Zamfara ba su zuwa makaranta a 2022. Amma kuma a 2018, kashin waɗanda ba su zuwa makaranta a yaran jihar, kashi 41.1 ne. Hakan na nuni da cewa lamarin ya fi taɓarɓarewa a zamanin Matawalle.
A 2020 yaran da ba su zuwa makaranta a Zamfara sun kai 422,214. Amma lissafin da Hukumar Kula da Ilmi a Matakin Firamare, UBEC, ta ce a ƙarshen 2022 yaran da ba su zuwa makaranta a jihar ya kai 883,953.
A ɓangaren kiwon lafiya, a 2019 akwai likitoci 300. Matawalle ya ƙara 50 sun kai 350 kenan a 2022.
Duk yawanci asibitocin jihar a Gusau su ke, sai ɗaiɗaiku a cikin ƙananan hukumomi.
A 2018, jinjirai 130 na mutuwa a cikin kowane ƙananan yara 1000 da aka haifa. Amma a yawan ya ƙaru zuwa yaro 136 a cikin 1000 da aka haifa. Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ce ta fitar da waɗannan bayanai.
Discussion about this post