Jam’iyyar APC ta roƙi Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi watsi da ƙararrakin da jam’iyyu uku masu jayayya kan nasarar Bola Tinubu su ka shigar.
Jam’iyyun dai su ne AA, APM da kuma APP.
APC ta roƙi Kotun Shari’ar Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa na 2023 cewa ta kori dukkan ƙararrakin uku da jam’iyyun su ka shigar daban-daban.
A ranar Lahadi ce lauyan APC Thomas Ojo ya shigar da ƙarar, wanda ya na cikin lauyoyin da ke kare APC a ƙarƙashin babban lauya Lateef Fagbemi, a Abuja.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa jam’iyya ta biyar ta garzaya kotu, ta ce Tinubu maguɗi ya yi, bai ci zaɓen 2023 ba.
Yayin da PDP, LP, AA da kuma APM duk su ka garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara kan rashin amincewa da nasarar APC da ɗan takarar ta Bola Tinubu a zaɓen 2023, jam’iyya ta cikon biyar mai suna APP (All Peoples Party) ta bi sahun su, ita ma ta garzaya kotu, inda ta ke jayayya da nasarar da Bola Tinubu da APC zu ka yi, ta zaɓen shugaban ƙasa ba 2023.
APP ta ce an ɗibga maguɗi a jihohi 11 inda aka bai wa Tinubu nasarar da bai cancanta ya samu ba.
Ɗan takarar APP mai suna Osita dai ya samu ƙuri’u 12,839, yayin da Tinubu ya samu miliyan 8.8, Atiku da ya zo na biyu, ya damu miliyan 6.9.
Shi kuma Peter Obi na LP ya samu miliyan 6.1.
Bayan ya bayyana yadda aka yi maguɗi a na sa zargin, Osita ya buga misalai a wurare daban-daban, sannan kuma ya kawo wasu dalilan da ya ce hujja ce mai nuna cewa Bola Tinubu bai cancanci fitowa takarar zaɓen ba ma baki ɗaya.
Daga cikin dalilan ko hujjojin sa, ya ce an yi tashe-tashen hankula a wasu yankuna, wasu wurare da dama kuma ba a yi zaɓen ba ma ɗungurugum.
APP ta ce zaɓen 2023 bai cika sharuɗɗan da Dokar Zaɓe ta 2022 ta gindaya ba.
Haka kuma a cewar sa, INEC ba ta tura sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a cikin Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe ta iReV daga cikin na’urar Tantance Masu Shaidar Rajistar Katin Zaɓe ba.
Ya ce a fam-fam ɗin da Tinubu ya cike na INEC, babu takamaiman sunayen garuruwan da ya yi karatu ko inda makarantun su ke
Cikin makon jiya ne jam’iyyyar Action Alliance (AA) ta ce wa kotu a soke nasarar da INEC ta ce APC da Tinubu su ka yi, a sake zaɓe.
Jam’iyyar ‘Action Alliance’ (AA), ta bi sahun PDP, LP da APM, inda ita ma ta garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayyana rashin amincewa da nasarar da APC da ɗan takarar ta, Bola Tinubu su ka yi na lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga Fabrairu.
AA ta roƙi kotu a sake zaɓe saboda INEC ba ta loda sunan haƙiƙanin ɗan takarar ta na Shugaban Ƙasa ba, Solomon David-Okanigbuan a manhajar hukumar zaɓen ba.
AA dai ta shigar da ƙara a ranar 16 Ga Maris, cewa duk da kotu ta bai wa INEC umarnin ta saka sunan halastaccen ɗan takarar ta na shugaban ƙasa, wanda hakan ya janyo wa jam”iyyar ta su asarar ƙuri’u masu yawan gaske.
Lauyan AA da Okanigbuan mai suna Dauda Usman, ya nemi a jingine zaɓen nasarar zaɓen da Tinubu ya samu, a sake wani sabo.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa an samu ƙarin jam’iyyar da ke jayayya da nasarar Tinubu, inda ta ce Asiwaju bai cancanci takara ba, a ƙwace a bai wa Atiku Abubakar na PDP.
Jam’iyyar ‘All Peoples Movement’ (APM), ta ce takarar Bola Tinubu na jam’iyyar APC da ya yi nasara, haramtacciya ce, domin ba a bi ƙa’iba wajen zaɓen ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Tinubu, wato Kashim Shettima.
APM ta bi sahun su PDP da LP, ta maka APC da INEC ƙara ranar 20 Ga Maris, ta na so Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓe a Abuja ta bayyana Atiku Abubakar a matsayin wanda ya zo na biyu, cewa shi ne ya yi nasara, kuma shi ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, ba Tinubu ba.
A ranar 1 Ga Maris ne aka bayyana cewa Tinubu ya yi nasara.
A cikin kwafen takardun ƙarar da APM ta shigar, ya ce Tinubu bai shiga takara bisa ƙa’ida ba, saboda Kashim Shettima bai cancanci tsayawa takara ba.
Idan ba a manta ba, lokacin da Tinubu ya fito takara, ya miƙa sunan Ibrahim Masari a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Ibrahim Masari ɗan Katsina ne, jihar Shugaba Muhammadu Buhari. An ajiye shi ne matsayin ɗan takarar wucin gadi, kafin zaɓen mataimaki, wanda aka ɗauki Shettima daga baya.
Masu sharhin siyasa maganin Tinubu ya ɗauki Ibrahim Masari ne don cika umarnin INEC cewa ranar 27 Ga Yuni ce za ta rufe karɓar sunayen ‘yantakara, wato ranar 17 Ga Yuni, 2022.
A ranar 10 ga Janairu Ibrahim Masari ya janye, Aka maida sunan Shettima.
A Daura Tinubu ya bayyana sunan Shettima matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, yayin da ya kai wa Buhari ziyasa.
A kan haka ne APM ta ce Shettima ya fito takara a wurare biyu, wato takarar sanata da ta mataimakin shugaban ƙasa a lokaci guda.
“Har zuwa ranar 25 ga Yuli, 2022, akwai sunan Tinubu a cikin masu takarar sanatoci.”
APM ta ce ta samu kwafen takarda daga INEC a ranar 14 Ga Yuli cewa a ranar an canja sunan Ibrahim, aka maye gurbin sa da na Ibrahim.
APM ta ce Sashe na 131(C) da 142 ya nuna Ibrahim Masari ne ɗan takarar mataimakin Tinubu, tunda ya janye kuwa, takarar Tinubu ta faɗi kenan.
APM ta ce Sashe na 131(C) da 142 na doka ya nuna Tinubu ba ɗan takara ba ne, domin ba ya halatta ya tsaya takara ba da mataimaki ba.
Waɗannan da wasu dalilai ne ya sa APM ta nemi kotu ta kwace nasara daga hannun Tinubu ta bai wa Atiku Abubakar na PDP da ya zo na biyu.
Discussion about this post