Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo da tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo na daga cikin ɗimbin manyan da su ka halarci jana’izar marigayi tsohon Ministan Shari’a, Bola Ajibola.
Ajibola wanda ya rasu a ranar Lahadi, an rufe a ranar. Ya rasu bayan rashin lafiyar da iyalan sa su ka danganta da tsufa.
Bayan an yi wa gawar sa sallah, bisa jagorancin Babban Limamin Egbaland, Sa’adallah Bamgbola, an rufe gawar a harabar Cibiyar Yaɗa Addinin Musulunci da aka fi sani da ‘Islamic Mission for Africa’ (IMA), wadda mamacin ya kafa shekaru da dama da su ka gabata, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Osinbajo da matar sa Dolapo sun isa wajen binne gawar misalin ƙarfe 4.57 na yamma.
Da ya ke magana muryar sa na rawa saboda jimamin rasuwar ogan na sa a ɓangaren shari’a, Osinbajo ya bayyana irin yadda ya yi aiki a ƙarƙashin mamacin tun cikin shekarun tamanoni (1980s).
Ya nuna jimami da baƙin cikin rashin mamacin wanda ya ce rashin sa ya babban rashi ne sosai.
“Na yi wa mamacin aiki a matsayin Mashawarci Na Musamman a lokacin da ya ke Ministan Shari’a. Mutum ne da ya yi amanna da kishi da tsananin ƙaunar ƙasar sa, kuma mai son a yi aiki da gaskiya, bisa ƙa’ida.
“Irin kusanci na da shi, ta kai zan iya cewa ni ne ma ɗan sa na fari, kamar yadda Segun ɗan na sa na fari ya faɗi.”
Sauran waɗanda su ka halarci jana’izar akwai Tsohon Gwamnan Ogun, Segun Osoba, Mataimakin Gwamnan Ogun, Noimot Salako-Oyedele da Cif Jojin Jihar Ogun, Mosunmola Dipeolu.
Akwai kuma sarakunan gargajiya da dama na yankin Yarabawa da su ka halarci jana’izar.
A ranar Lahadi ce dai Tsohon Ministan Shari’a, kuma tsohon Shugaban Kotun Ƙasa da Ƙasa, Bola Ajibola ya rasu.
A cikin alhini an bayyana rasuwar tsohon Mai Shari’a a Kotun Duniya, kuma tsohon Ministan Shari’a, Bola Ajibola.
CIkin wata sanarwar da babban ɗan sa Segun Ajibola ya sa wa hannu, kuma ya fitar, ya ce Ajibola ya rasu a Abeokuta, ranar Lahadi.
“Mu na baƙin ciki, jimami da alhinin rasuwar mahaifin mu Prince Bola Ajibola. Allah ya ba shi rabon aljanna, Amin.”
Ajibola wanda tsohon Ministan Harkokin Shari’a ne, ya rasu ya na da shekaru 89 a duniya. Ya rasu bayan fama da rashin lafiyar da ke da alaƙa da tsufa ko yawan shekaru. Kamar dai yadda iyalan na sa su bayyana.
Ya yi Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Ƙasa daga 1984 zuwa 1985.
Kuma ya kasance ɗaya daga cikin Kwamishinonin Hukumar Shata Kan Iyakar Eritrea da Habasha, wadda Kotun Duniya ta shirya a lokacin.
Tsakanin 1999 zuwa 2002 kuma, Ajibola ya zama Jakadan Najeriya a Birtaniya.
Shi ne ya kafa Jami’ar Cresent University a Abeokuta, da kuma Cibiyar Bunƙasa Musulmi ta Afrika, IMA.
Discussion about this post