Jam’iyyar APC Reshen Jihar Ribas, ta ƙaryata wani rahoton da wata kafar yaɗa labarai ta ce tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya kira zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu da suna ‘dillalin muggan ƙwayoyi’.
Kakakin APC na Ribas, Darlington Nwauju ne ya fitar da wannan sanarwar a ranar Juma’a, ya na cewa a matsayin Amaechi na tsohon Gwamnan Ribas, tsohon Ministan Sufuri, kuma jagoran APC yanzu haka a Jihar Ribas ɗin, bai taɓa kiran Tinubu da sunan ‘dillalin muggan ƙwayoyi’ a cikin Najeriya ko a ƙasashen waje ba.
Nwauju ya yi wannan raddi ne biyo bayan wata kafar yaɗa labarai ta wallafa a shafin ta na Facebook mai suna Dailymail gist cewa “Amaechi ya ce Tinubu dillalin muggan ƙwayoyi ne.”
Jaridar ta ce, Ameachi ya ce, “Idan da APC da INEC sun yi bincike mai zurfi, to kuwa da sun hana Tinubu tsayawa takarar shugaban ƙasa, saboda laifin safarar muggan ƙwayoyi.”
Sanarwar ta ce Amaechi bai taɓa furta wannan magana ba, bai kuma zai yarda ya furta hakan ba. “Aikin wasu shaiɗanu ne waɗanda ba su neman Amaechi da alheri, sai sharri kawai.”
Idan ba a manta ba, Amaechi ya bayyana cewa bai kamata a sake naɗa Shugaban INEC, Mahmood Yakubu kan muƙamin sa ba.
Ya yi wannan furuci ne yayin da ya ke ganawa da manema labarai jin kaɗan bayan ya jefa ƙuri’a a zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihohi, a ranar 18 Ga Maris.
Discussion about this post