Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa ya fara danƙara wa bankunan kasuwanci maƙudan takardun kuɗaɗe a faɗin ƙasar nan.
Daga nan kuma ya umarci bankunan su riƙa aiki har Asabar da Lahadi, domin su wadatar da kuɗaɗe ga jama’a baki ɗaya.
Sanarwar da Kakakin Riƙo na CBN, Isa Abdulmumin, ya ce shirin wani ƙoƙari ne da CBN ke yi domin wadatar da ƙasar nan da takardun kuɗaɗe daban-daban.
Duk da sanarwa ko umarnin a ci gaba da amfani da tsoffin Naira 200, 500, 1000, har yau ana ci gaba da ƙarancin takardun kuɗaɗe a faɗin ƙasar nan.
A yanzu takardun kuɗaɗe sabbi da tsoffin duk sun yi ƙaranci, sai an saya kamar yadda ake sayen dala a kasuwar ‘yan canji.
A ranar Juma’a CBN ya ce ya danƙara wa bankunan kasuwanci maƙudan kuɗaɗen da za su riƙa bai wa kwastomomi, yadda za su wadatu a cikin ƙasa.
Isa ya ce CBN ya umarci bankunan kasuwanci su riƙa ɗura kuɗaɗe cikin ATM domin kwastomomi su riƙa cira.
Haka nan sanarwar ta ce Gwamnan CBN Godwin Emefiele da kan sa zai riƙa zagayawa domin gane wa idanun sa bankunan da ke bijire wa doka.
Discussion about this post