Ɗan takarar zaɓen shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa APC na shirya tuggun hargitsa zaɓen shugaban ƙasa, ta hanyar ƙoƙarin haddasa rikice-rikice don ta tilasta wa INEC ɗage zaɓe a wasu yankuna.
Atiku ya ce tuggun da APC ke shiryawa shi ne a ɗage zaɓe a wasu wurare a faɗin ƙasar nan, ta yadda ba za a iya gudanar da zaɓe lokaci ɗaya a faɗin ƙasar nan ba.
Cikin wata sanarwa da Hadimin Yaɗa Labaran Atiku, wato Prank Shuaibu ya fitar, ya yi gargaɗin cewa idan aka kasa gudanar da zaɓe a lokaci guda a ƙasar nan, wato a rana ɗaya, to ana so ne kawai a yi maguɗi.
Ya ce rikicin da aka yi a Kano alama ce mai nuni da wannan tuggun da APC ke shiryawa.
“A yau an yi mummunan rikici a Kwanar Ɗangora, wajen Kano, kan hanyar Zaria. Jiha ce da APC ke mulki. Sun fara da hargitsi kamar yadda su ka yi cikin 2019, inda su ka yi amfani da tashin hankali su ka koma kan mulki da tsiya-tsiya.
“Mun kuma ji labarin cewa irin haka zai faru a Barno, Yobe, Kaduna. Dama Kaduna ita na ta na musamman ne, domin Gwamna El-Rufai na ta ingiza mutane su bijire wa Shugaba Muhammadu Buhari. Ya ruɗe, ya gigice tun da ya ga abin da ya shirya kan tsoffin kuɗi bai yi nasara ba.”
Shuaibu ya jinjina wa ‘yan sanda saboda kama wani ɗan Majalisar Tarayya wanda Ephraim Nwuzi, wanda aka watsa bidiyon da aka nuni shi ya na tattauna yadda za a kai wa jami’an zaɓe hari a Jihar Ribas.
Discussion about this post