Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah Wa Bara Ka Tuh
Tabbas Malamai suna da kima da daraja da matsayi mai girma ba kadan ba a cikin al’ummah. Domin Allah Subhanahu wa Ta’ala da kansa, shine ya tabbatar da wannan daraja da matsayi a gare su. Ya fada a cikin littafinsa mai girma Alkur’ani, cewa yana daga darajar wadanda suka yi imani daga cikinku, da wadanda aka bai wa ilimi da wata daraja ta musamman. Sannan Allah Ta’ala ya fada cewa lallai masu jin tsoron Allah a cikin bayinsa, su ne malamai.
A takaice dai, malaman addini ba karamar daraja da girma suke dashi ba a wurin Allah da kuma bayin Allah. Amma abun bakin ciki, duk wanda yake bin al’amurran da ke faruwa yau a kasar mu mai albarka Najeriya, tabbas, zai yarda dani idan nace lallai akwai wasu daga cikin gurbatattun ‘yan siyasa wadanda suke kokarin zama sanadiyyar zubewar wannan daraja da Allah yayi wa malamai magada Annabawa.
Misali, ai ina ganin kowa yasan da cewa irin wannan tsari na gudanar da shugabanci a karkashin dimokradiyyah ba tsari bane na Musulunci, don haka kenan mu al’ummar Musulmi muna yin sa ne a bisa babi na lalura. To sai gashi wasu daga cikin malamai suna kokarin nuna cewa idan kayi wata jam’iyyah kayi Musulunci, idan kuma kayi wata jam’iyyar baka yi Musulunci ba.
Kai abun yayi kamari sosai, har wasu malaman suna kokarin kafirta ‘yan uwansu Musulmi, saboda kawai basu yin jam’iyyah daya, ko kuma basu goyon bayan dan takara daya.
Ya ku ‘yan uwana masu girma, ina mai shaida maku cewa, duk jam’iyyun nan babu wata jam’iyyah ta Musulunci a cikin su. Kuma babu wata jam’iyyah da za’a ce cin nasarar ta cin nasarar Musulunci ne, ko faduwar wata jam’iyyah faduwar addinin Musulunci ne. Ko kuma ace idan wani dan takara cikin ‘yan takara yaci zabe addinin Musulunci ne yaci zabe, idan kuma wani dan takara ya fadi zabe addinin Musulunci ne ya fadi. Ina mai yi maku rantsuwa da Allah, wannan ba gaskiya bane.
Domin duk cikin ‘yan takarar nan, babu wanda idan yaci zabe zai yi aiki shari’ar Musulunci, ko yayi aiki da littafin Allah da Sunnar Manzon Allah (SAW). Dukkanin su duk wanda yaci zabe da kundin tsarin mulkin Najeriya ne zai gudanar da mulkinsa.
Don haka kenan yanzu magana ce cancanta, da kuma wa yafi dacewa ya shugabanci kasar nan, kasa mai al’ummomi har sama da miliyan dari biyu. Wanda Allah zai yi amfani da shi domin ciyar da kasar nan da al’ummarta gaba.
Sannan abun da ya kamata dukkaninmu mu fahimta shine, Najeriya kasa ce wadda Allah ya hada Musulmi da Kirista a cikinta. Kuma dukkanin mu ‘yan kasa ne. Kuma ko mun ki, ko mun so dole mu zauna tare. Ba mai iya korar wani daga cikin ta. Tun da haka ne, abun da yake mafi dacewa shine, muyi kokarin fahimtar hanyoyin zaman lafiya da juna.
Abun bakin ciki, a yau an wayi gari wasu daga cikin kiristoci suna amfani da addininsu wurin cimma wani buri nasu na kashin kansu da sunan siyasa. To kuma sai wasu daga cikin ‘yan uwan mu Musulmi, musamman wasu malamai da limamai abun mamaki, sai suka biye masu, suma suna amfani da addinin Allah, wurin cimma nasu burin na siyasa.
Wallahi, wallahi, wallahi duk wannan bai dace ba. Kuma mu sani, daga kiristocin har Musulmin, wadanda duk suke amfani da addini ta wannan hanya, suna tunzura ‘yan kasa, duk suna kan kuskure babba, wanda zai iya jefa kasar nan cikin babban tashin hankali, da rudani, da hayaniya, wanda Allah ne kadai yasan inda zai tsaya.
Addinin Allah alkhairi ya kawo wa duniya. Bai kawo wa duniya husuma, hada fada, da yada damuwa da tashin hankali tsakanin mutane ba.
Sannan irin wannan kawo maganar addini cikin kamfen din, da fadin maganganun da basu dace ba, da harzuka ‘yan kasa, shine ya taba haddasa mummunan tashin hankali da rikici a jihar Kaduna, a lokacin shugaba Jonathan, inda aka kashe dubban Musulmin da Allah ne kadai yasan adadin su!
Don haka ya zama wajibi a bar mutane su zabi ra’ayinsu, ba tare da an tursasa su ba.
Sannan don Allah ta yaya zamu mayar da addinin Allah haka da arha, har ‘yan siyasa suna tara mu, suna bamu dubu hamsin-hamsin ko dubu dari-dari, wai don mu isar da sakon da suke bukata ga al’ummah? Haba don Allah, kana nufin wannan kudin zai magance maka talauci ne?
Jiya, a jihar Zamfara an tara wasu daga cikin Sarakuna, hakimai, dagatai, masu anguwanni, limamai da malamai, domin ayi amfani da su, a tursasawa jama’ah zaben wani dan takara, ko da ya sabawa ra’ayinsu da ra’ayoyan al’ummominsu.
A jihar Kano, yanzu da yamman nan, aka tara wasu limaman juma’ah da wasu malamai, aka karbi sunayensu, da lambobin wayoyinsu, da lambar asusun ajiyar su na banki (account number), aka ce dasu gobe juma’ah idan Allah ya kai mu, ana so suyi hudubobin juma’ah, su sanar da al’ummah cewa tikitin Muslim-Muslim addini ne, akasin haka kuwa kafirci ne. Sannan sharadin da aka sa masu shine, ba za’a tura maka kudi a asusun bankin ka ba, har sai kayi hudubar da ake so goben, sannan ka turo bidiyon hudubar, sai a aika maka da sakon kudi ta asusun bankin ka.
Haka fa suke ta yi a sauran jihohin, suna amfani da limamai da malamai magada Annabawa, domin kai wa ga mulki kota-halin-kaka.
Haba Malamai magada Annabawa! Don Allah haka zaku yi kokarin zubar da darajar da Allah yayi maku? Ai addinin Allah yafi karfin ayi wasa da shi haka.
Sannan don Allah, kai a matsayinka na limami ko malami, don Allah baka san irin hudubar da ya kamata kayi wa al’ummah ba, har sai wani dan siyasa ya cusa maka ra’ayinsa, ko yace da kai ga abun da yake so ka fada a hudubar?
‘Yan siyasar nan fa sun sha fada cewa, malamai ne kadai suka rage masu mutunci a cikin al’ummah. To me yasa suke kokarin zubar maku da wannan mutuncin?
Kuma wani abun bakin cikin shine, ‘yan siyasar nan ba su tuna wadannan malamai masu daraja sai a irin wannan lokacin. Da zarar an gama siyasa, ba zasu sake neman su ba.
Kuma a yau an wayi gari cewa, duk wani limami, ko malamin da yace bai yarda da ra’ayinsu ba, sai su kira shi da sunan munafuki ko kuma makiyin addinin Musulunci.
Sannan Allah Subhanahu wa Ta’ala ya fada muna cewa idan mun ji tsorosa, to duk wani makircin kafirai ba zai cutar da mu da komai ba, amma wasun mu suna ta kokarin fada muna akasin haka! Suna ta tsoratar da bayin Allah sharrin kafirai, amma ba zasu tsoratar da su game da Allah mahaliccinsu ba. Alhali mu mun sani, BABU WANI KAFIRI DA ZAI IYA YIWA MUSULUNCI DA MUSULMAI WATA ILLA, MATUKAR MUSULMAN SUN JI TSORON ALLAH MAHALICCINSU!!!
Sannan kuma mun sani, daukakar addinin Musulunci da Musulmai yana da alaka ne da rikon su da addinin Allah din, ba faduwar wata jam’iyyah ba, kuma ko wace jam’iyyah ce, ko kuma faduwar wani dan takara ko wanene shi.
Daga karshe ina mai roko, don Allah iyayen mu malamai magada Annabawa, kuyi kokari kuci gaba da rike matsayinku da mutuncinku. Kar ku yarda wani dan siyasa ya zubar maku da wannan daraja da Allah ya baku.
Sannan don Allah ina rokon ku, ku bar yin amfani da addinin Allah ta inda bai dace ba.
Gobe Juma’ah idan Allah ya kai mu, kar kuce za kuyi hudubobin da zasu zama sanadiyyar rarrabuwar jama’ah da sunan yiwa wani dan takara kamfen. Domin tabbas, yin hakan zai iya jawo zubewar mutuncinku a wurin jama’ah, kasancewar ba ‘ya ‘yan jam’iyyah daya ne suke sallah a masallatanku ba.
Idan kuma zaku yi maganar siyasa, to ku fada wa mutane su zabi cancanta; su zabi shugaban da ya dace, mai hankali, mai lafiya, wanda zai amfani al’ummah, ba wanda zai zamar masu alakakai ba, ba kuma wanda za’a yi dana-sanin zaben sa ba!
Sannan don Allah ina rokon ku, da ku taimakawa kan ku, ku taimaki kasar ku, ku taimaki shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya gudanar da zabe mai inganci, wanda kowa zai ji dadin sa.
Kuma kar kuce sai an baku kudi sannan zaku zabi shugaba nagari.
Daga karshe, ina addu’a, Allah yasa mu dace da zaben shugabanni nagari, yasa mu tsira da mutuncinmu, duk halin da ake ciki, amin.
Wassalamu Alaikum
Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.