Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo ya caccaki sabon tsarin sauya launin kuɗin da CBN ya ƙaƙaba wa ‘yan Najeriya, wanda ya ce haka kawai an wayi gari an haifar wa al’ummar ƙasar nan wahalhalu na ba gaira babu dalili.
Osinbajo ya yi wannan damuwa ce a lokacin da ya karɓi masu ziyara daga Ƙwararrun masanan fasahar hada-hadar zamani ta FinTech, waɗanda ya gana da su a ranar Juma’a, a Abuja.
“Mutum ya na buƙatar kuɗi a aljihun sa domin shiga motocin sufuri. Misali a Abuja ya mutum zai riƙa hawa motar haya idan babu kuɗi aljihun sa?
“Ta yaya mutum zai sayi kayan abincin yau da kullum idan babu kuɗi a cikin aljihun sa? Ko sayen katin waya ma jidali ne idan mutum ba shi da ko kwabo a aljihu.” Cewar Osinbajo.
“Iyayen yara kullum safiya sai sun bai wa yara kuɗin tafiya makaranta, kuɗin abinci a makaranta da kuɗin motar komawa gida. Saboda haka ana buƙatar kuɗaɗe a aljihu a kullum domin magance matsalolin yau da kullum.” Inji Osinbajo.
Osinbajo ya yi kira ga CBN da sauran bankuna su yi aiki tare da FinTechs masu ejan na hada-hadar kuɗaɗe domin wasu samar wa jama’a sauƙi a faɗin ƙasar nan.
A ranar Juma’a ɗin ce kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Gwamnonin APC, dangane da illar da sauya launin kuɗi ya haifar a faɗin ƙasar nan.
A wurin, Buhari ya ce ba zai yi wa zaɓen 2023 katsalandan ba.
Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada wa Gwamnonin APC cewa ba zai yi wa zaɓen 2023 katsalandan ba.
Ya yi masu wannan bayani ne a ranar Juma’a, lokacin da su ka kai masa ziyara, domin su nuna masa halin da ƙasar nan ke ciki sanadiyyar sauya launin kuɗi.
Da ya ke masu jawabi, Buhari ya kafa masu hujja da buga misalai da cewa:
“Mun tabbatar kuma mun ga abin da ya faru a zaɓukan Anambra, Ekiti da Osun. Abin da ya faru a waɗannan jihohi ya ƙara min ƙwarin guiwar cewa mu na samun gagarimar nasara.”
Da ya koma maganar wahalhalun da jama’a ke sha, ya roƙi ‘yan Najeriya su ba shi wa’adin mako ɗaya domin ya shawo kan matsalar ƙarancin sabbin kuɗaɗe a hannun jama’a.
Ya ce maƙasudin kafa sabon tsarin hada-hadar kuɗaɗen ba don a ƙaƙaba wa jama’a wahala ba ce, sai don a sauƙaƙa wa mutane rayuwa ta hanyar tasarifin kuɗaɗe a sauƙaƙe.
Sai dai kuma ya zargi wasu bankuna da laifin kawo cikas a lamarin, inda ya ce “wasu bankunan ba su da babban jari sosai, saboda haka kan su kawai su ka sani.”
Buhari ya ce ya nuna damuwa ganin yadda ya kalli fayafayen bidiyon yadda mutane ke wahala a bankuna wurin ƙoƙarin cirar kuɗi a cikin bankuna a kuma a na’urar ATM.
Ya ce zai gana da CBN da kuma Kamfanin Buga Kuɗaɗe na Najeriya domin a fuskanci gaskiyar lamarin.
Sai dai kuma duk da gwamnonin sun nuna wa Buhari goyon bayan sabon tsarin da kuma sauya launin kuɗaɗe, sun nuna masa irin halin da jama’a su ka tsinci kan su sakamakon canjin kuɗaɗen.
Sun nuna masa tsoron cewa wahalar da jama’a ke ciki za ta iya shafar nasarar jam’iyyar su a zaɓen 2023.
Daga nan Gwamnonin sun roƙi Buhari ya yi magana a wadata bankuna da sabbin kuɗaɗe, kuma a ci gaba da karɓar tsoffin ana hada-hada da su, daga nan har ƙarshen shekara.
Buhari ya ce kafin a fara buga kuɗin, ya ce kada a sake a buga su a ƙasar waje, sai dai a buga a cikin Najeriya. Ya ce an kuma tabbatar masa cewa za a iya buga wadatattu a cikin ƙasar nan.
A ƙarshe ya ce dalili kenan zai zauna da CBN da Kamfanin Buga Kuɗi domin ya gano gaskiyar lamarin.
Discussion about this post