Rundunar Kamfen din dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi sun maida wa gwamnan Kaduna da martani cewa maimakon cika baki da yaki yi a kafafen yada labari, abinda ya fi dace masa shine ya yi gaggawar komawa ga Allah ya nemi gafarar sa kan bala’o’in da ya gallaza wa mutanen Jihar Kaduna.
Idan ba’a manta ba El-Rufai ya bayyana a hira da yayi da talbijin din Channels cewa Peter Obi yan a batya ruwa ne kawai amma ba tsairin da za suyi a zaben shugaban kasa da ya karato a kasar nan.
El-Rufai ya ce Obi na yin amfani da kabilanci da addini ne a wajen neman jama’a wanda hakan ba zai sa ya samu abinda yake so ba a zabe mai zuwa.
A martani da rundunar suka maida wa gwamnan, Darekta janar din rundunar Kamfen din Obi Akin Osuntokun ragargaji gwamnan inda yake cewa shine gogarmar nuna kiyayya da kabilanci, domin shine ya fara yin haka a Kaduna inda ya yakice wani bangaren jihar ya kirkiro takarar muslim-muslim.
” Ina so in sanar wa El-Rufai, idan aka da sahihin zabe a kasar nan, tabbas Obi na LP ne zai yi nasara, ko shakka babu. Abu daya da na sani shine ko Obi ya yi nasara ko bai yi nasara ba ya kafa tarihi a kasar nan.