Wasu ‘Yan bindiga sun kai hari tashar jirgin ƙasa da ke ƙaramar hukumar Igueben a jihar Edo tare da yin garkuwa da fasinjoji masu yawa.
Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne a daidai lokacin da fasinjojin ke shirin hawa jirgin ƙasan zuwa garin Warri da ke jihar Delta.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Edo Chidi Nwabuzor, ya ce ba samu labarin rasa rai ko daya ba.
Sai dai kuma Nwabuzor ya tabbatar da cewa wasu fasinjojin sun samu raunukan harbin bindiga.
Ya ce maharan sun far wa tashar jirgin ne da yammacin ranar Asabar, inda suka yi kan mai uwa dawabi suna harbi a sama kafin su kama wasu da yawa daga cikin fasinjojin.
Wannan lamarin na zuwa ne ƙasa da shekara guda bayan da ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ‘yan ƙungiyar Boko Haram sun kai hari kan jirgin ƙasan Abuja- Kaduna a arewacin ƙasar tare da yin garkuwa da fasinjoji masu yawa, inda suka kwashe tsowon watanni a hannun ‘yan bindigar.
Discussion about this post