A Yau yadda Jami’oin Nijeriya suka tada kudin makaranta, tashin gwauran zabi, ba wani abin mamaki bane ganin yadda a ka kai ruwa rana, tsakanin gwamnatin tarayya da Kungiyar Malaman Jami’oi wato ASUU, a kwanakin baya, kuma a ka juyawa ASUU baya kan wannan lamari.
In Yan Nijeriya za su tuna dama Shugaban Kasa Buhari yayi wannan bayani a gaban Majalissar Dokoki yayin da yake gabatar da Kasafin kudin wannan shekarar, ya nuna cewa gwamnatin tarayya baza ta iya cigaba da daukan nauyin karatun manyan makarantu ita kadai ba.
In ha’ila yau ‘Yan Nijeriya za su sake duba da dokar da Majalissar Dokoki tayi, Mai Lamba HB 1998 ta ranar 23 ga watan 11, shekarar 2022, wanda ta sanya cewa dole Dalibai suna biyan kudi (tuition fees) a duk manyan makarantu mallakar gwamnatin tarayya da al’amuran masu kama da haka.
To, daman wannan yunkuri ba yanzu gwamnati ta soma yin sa ba, amma yan Nijeriya sun gaza fahimtar haka, kawai Malaman Jami’oin Nijeriya ne wato ASUU suke dagewa da kin yarda da wannan manufar tattalin gwamnati.
Koda a wannan Yajin Aikin da suka yi na bayan nan, wanda har aka hana su albashin su na tsawan wata takwas, sun jajirce a kan cewa gwamnati sai ta inganta Jami’oin nan, sun nuna wa gwamnati cewa, Nijeriya na da arzikin daukan nauyin Jami’oin kasar nan.
Amma, abin takaicin shine hatta Daliban da Iyayen su da Yan ASUU suke ta rigima a kansu, sun gaza bahimtar wannan matsalolin da suke hangowa.
Mutane da dama sun kasance suna sukar ASUUn da Takwarorin ta na Jami’oin Nijeriya a kan jajincewar su, sai gwamnati ta sauke nauyin ta a kan matsalolin Jami’oin ta.
Shin a irin wannan tsarin Dan Talakawa kenan an kange shi daga samun karatun JAMI’A? Ko da kuwa shine burin sa a rayuwa?
Ba wai kawai Talakawa ne suka samu kansu a wannan masifa, hatta ‘Yan Nijeriya masu karamin samu fa, suma suna tsaka mai wuya. Musamman mu ‘Yan Nijeriya masu tara iyalai da yawa.
Wannan matsayi fa, ba kawai Talakawa zai shafa, hatta Tattalin Arzikin Nijeriya da Hukumomin Ilimi da kiwon Lafiya sai sun sami tasgaro.
Domin Dan Talaka ne zai iya aikin jinya, Dan Talaka ne zai iya aikin Malamin Makaranta, Koma kananan aiyuka da su suke bunkasa tattalin arzikin kasa.
Ko ba komai, a yau duba da karayar tattalin arzikin mutanen kasar nan da karuwar talauci ga al’ummah, zai yi wahala mafi yawa da ga mutanen kasar nan masu burin yin karatun Jami’a burin su ya cika.
Ko a kwai mafita?
Zai yi wahala a ce, an koma kamar da, ganin yadda Gwamnatin Buhari tayi daurin tankila a kan wannan matsalar. Anyi doka, kuma gwamnati ta bawa Jami’oin ta ikon cin kashin kawunan su.
Dadi da kari kuma Gwamnati, Dalibai da iyayen su sun sarewa Kungiyar Malaman Jami’oin Nijeriya ASUU kafa, sannan Kungiyar Dalibai a Nijeriya basu da karfin yin wannan fafiti ka.
Wannan al’amari hatsari ne, ba kawai ga ‘Yan Nijeriya, hatta GA Nijeriyar kanta.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post