Mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Omo-Agege ya yi alkawarin baiwa kowa ƴancin sa ba tare da nuna banbanci ba idan ya zama gwamnan jihar a 2023.
Omo-Agege ya bayyana haka ne a lokacin da yake yawan kamfen a wasu yankuna dake babban Warri.
Ya ce ” Idan na zama gwamnan jihar Delta, ba za a nuna wa musulmi ko kuma wanda ba musulmi ba banbanci a jihar. Sannan kuma babu nuna wariya na kabilanci. Idan makaranta ne, kowa zai biya kuɗin makaranta daidai da wanda ake biya ne babu banbanci.
” Haka kuma aiki, idan za a dauki ma’aikata aiki, ya a baiwa kowa dama ba za a nuna banbanci ko fifiko ga wasu ba wai don ko addinin su ko kuma kabilar su.
Omo-Agege ya kara da cewa jihar Delta ta kowa ce, bai ga dalilin da za a rika nuna wa wasu banbanci ba saboda ko addini ko kuma na kabilanci duk da kuma suna biyan haraji a jihar daidai da kowa.
A karshe sanatan ya gargaɗi ƴan wasu jam’iyyu a jihar cewa kada wani ya kuskura ya ce zai muzguna wa ɗan jam’iyyar APC a jihar ta hanyar wata barazana ko kuma nuna fin ƙarfi a lokacin zaɓe.
” Idan aka ce za a yi wa mutanen mu haka, za mu ɗauki matakin gaske akai. Saboda haka duk yadda kowa ke da iko a fadin jihar haka muma mutanen mu ƴan APC ke da irin wannan iko.
Discussion about this post