Sojojin dake aiki karkashin rundunar ‘Operation Hadin Kai (OPHK)’ sun kama ‘yan ta’adda 79 tare da wasu masu yi musu hidima a cikin makonni biyu da suka gabata a yankin Arewa maso Gabas.
Darektan yada labaran hukumar tsaron Najeriya manjo-janar Musa Danmadami ya sanar da haka a Abuja da yake bada bayanan nasarorin da dakarun suka yi a aikin samar da tsaro a cikin makonni biyu da suka gabata.
Danmadami ya ce a wani harin da dakarun sojin sama da kasa suka kai wa ƴan ta’adda sojoji sun ceto mutum 14 da aka yi garkuwa da su, ciki akwai mata biyu da aka yi garkuwa da su daga Chibok.
Ya ce matan Chibok din da suka ceto sun hada da Yana Pogu da Rejoice Senki tare da ‘ya’yan su a kauyen Bula Davo dake karamar hukumar Bama da kauyen Kawur dake karamar hukumar Konduga duk a jihar Borno.
Danmadami ya ce dakarun sun kama mutum 29 dake yi wa Boko Haram/ ISWAP hidima.
Ya ce dakarun sun kama wadannan mutane da manyan buhunan busashen kifi 50, manyan buhunan busashhen nama biyu, jarka 55 na man fetur, kudi Naira miliyan ₦2.4 da wasu kaya.
Ya kuma ce dakarun sun kama wani mutum dake kera bindigogi da harsasai a kauyen Gorom dake karamar hukumar Monguno a Borno.
Danmadami ya ce sojojin sun kama mutum shida masu yi wa ‘yan ta’adda hidima inda a ciki akwai wani da ba dan Najeriya ba ne.
An kama su da bindiga kirar AK-47 guda shida, harsasai da dama, bindiga kirar HK guda daya, da G3 daya, harsasai 112, shanu 285 da galan 8 na man fetur.
“Dakarun sun kashe ‘yan ta’adda 19 sun kama mutum 42 da ake zargin ƴan aiken Boko Haram ne, sannan sun ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su.
“Wasu tubabbun Boko Haram tare da iyalen su guda 428 sun mika wuya, ciki akwai maza 44, mata 135 da yara kanana 239.
Ya ce a ranar 23 zuwa ranar 28 ga Satumba rundunar sojin sama dake aiki a karkashin OPHK sun gano mabuyar ‘yan ta’adda a kauyukan Kolaram da Bukar Meram dake Kudancin tafkin Chadi a jihar Borno.
Sojojin sun kashe ‘yan ta’adda da dama a wannan hari.
Danmadami ya ce rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ dake Arewa maso Yamma sun kashe ‘yan ta’adda biyar sun kama wasu 7 sannan sun ceto mutum 8 da aka yi garkuwa da su a cikin mako biyu.
Dakarun sun kuma yi wa wasu ‘yan ta’adda ruwan bama-bamai a sansanin Gwaska Dankaramis dake kauyen Mashekari a karamar hukumar Zurmi da sansanin Sani Dangote dake kauyen Farara a karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.
Danmadami ya ce dakarun sun samu nasarar kashe wani dan ta’adda Dogo Rabe da mabiyansa bakwai a wannan harin.
Discussion about this post