Kungiyar malaman sakandaren jihar Kaduna ASUSS ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe malamai 10 sannan sun yi garkuwa da sama 50 daga watan Janairu zuwa Oktobar 2022.
Shugaban kungiyar NUT, Audu Amba ya sanar da haka yayin da ya ke yin jawabi a wurin taron ranar malamai da aka yi a filin taro na eagle square dake Abuja.
Ya ce ” Irin matsalolin da fannin ilimi ke fama da su a Najeriya sun haɗa da rashin isassun malamai, rashin wuraren aiki, rashin karin girma da kum isassun kuɗade domin tafiyar da harkar Ilimi a jihar da kasa ba ki ɗaya.
A taron da ya yi da manema labarai a ranar malamai ta duniya shugaban kungiyar ASUSS na jihar Kaduna Ishaya Dauda ya ce ‘yan bindiga sun kashe malamai 10 sannan sun yi garkuwa da akalla malamai 50 daga watan Janairu zuwa Oktoba.
Dauda ya ce a jihar Kaduna malamai sun fi fama da rashin tsaro fiye da duk wani abu. Sai dai kuma ya yaba wa gwamnati bisa kokarin da take yi na ganin ta samar da tsaro a jihar.
“Kungiyar ta kuma mika godiyarta ga gwamnan jihar Nasir El-Rufa’i na biyan albashin malamai kan lokaci.
Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnan da ya yi kokari ya biya fansho da kudin sallaman malaman da suka daina aiki a jihar domin rage wahalan rayuwa da wasun su ke fama da su.
ASUSS ta yi kira ga El-Rufa’i da ya kara wa malaman albashi da karin girma.
Discussion about this post