Wani soja da ya je sasanta rikici tsakanin wasu makiyaya da manoma a karamar hukumar Guri jihar Jigawa ya gamu da ajalinsa a wurin rabon gardama.
Wannan abin takaici ya auku ne ranar Laraba a lokacin da soji suka kai agajin gaggawa domin sasanta rikici da tsakanin makiyaya da manoma a kauyen Gajiya.
Mazaunan kauyen sun ce Sojan, mai suna Danlami Danjuma na daya daga cikin sojojin da suka zo kauyen domin sasanta rikicin.
Mazauna sun ce makiyayan da suka tada rikicin ne suka kashe Danjuma sannan suka arce da bindigarsa.
Shugaban karamar hukumar Musa Muhammad ya ce mutane da dama musamman fulanin dake zaune a karamar hukumar sun yi tir da abin da ya faru.
Muhammad ya ce yanzu lokacin ne da makiyaya ke neman wuraren da dabbobin su za su riƙa kiwo saboda fama da ambaliyar ruwan da aka yi fama da shi a yankunan jihar.
“A dalilin haka ya sa makiyaya kan kora dabbobin su cikin gonakinsu
“Muna zargin cewa makiyayan da suka aikata wannan kisa baki ne ba ƴan asalin jihar ba.
Ya ce sojoji tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro na farautan makiyayan domin kamo su da kwato bindigar da suka arce da shi.
Discussion about this post