Gwamnan jihar Ribas Nyesome Wike ya naɗa sabbin hadimai 28,000.
Waɗannan nadenade sun zo ne a matsayin ƙari ga wasu hadiman da ya naɗa a kwanakin baya su 14,000.
Bayan haka gwamnan ya naɗa wasu mutum 319 da za su rika ganawa da mutane a madadin gwamnati a mazaɓu da wasu mutum 40 a kananan hukumomi.
Kakakin gwamna Wike Kelvin Ebiri ya ce naɗe naɗen da gwamnan yayi ya sun aiki nan take.
Ebiri ya ƙara da cewa gwamna Wike ya baiwa waɗanda amabliyar ruwa yayi wa ta’adi tallafin naira biliyan ɗaya.
Har yanzu ba a san inda Wike da maƙarraban sa suka sa kai ba a siyasar 2023.
Tun bayan faduwa zaɓen fidda gwani da yayi a PDP, ya ja layi tsakanin sa da ɗan takarar da yayi nasara, wato Atiku Abubakar.
Yana nan a PDP amma kuma kurwar sa ta na wani wurin da haryanzu ba a san wace reshen ya kama ba.
Discussion about this post