Kakakin ‘yan sandan jihar Zamfara Mohammed Shehu ya bayyana cewa rundunar ta kama wasu mutum 10 da ke aiki yi wa ‘yan bindiga aiki a fadin jihar.
Shehu ya ce rundunar ta bi sawun wadannan mutane ne har Allah ya basu sa’an cafke su.
Sune suke yi wa ‘yan bindigan dake kai harehare a yankunan kananan hukumomin Gusau, Kaura Namoda, Tsafe, da Bungudu.
” Wani daga cikin wadanda aka kama Abubakar Mainasara ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun biya shi naira 850,000 ya siya musu kayan sojoji. Kuma ya baiwa wani tela da yake dinka musu kayan. Sannan kuma sun biya naira miliya 2 ya siyo musu harsasai da da kayan aiki.
Shehu ya kara da cewa an kama wani wani Zainu Lawal, wanda shima aikin sa samar wa ‘yan bindiga kayan sojoji ne da kuma hassasai da kayan aiki. Sannan kuma ya ce a da shine ya ke gyara musu babura idan suka lalace a daji. Kuma yakan yi musu jigilar abinci da kayan amafani na yau da kullum.
A karshe Shehu ya ce za a maka su akotu da zarar an kammala bincike akan su.
Sojojin Najeriya sun kara kaimi matuka a kokarin kawo karshen hareharen yan bindiga a kasar nan.
Jihar Zamfara ce kan gaba wajen fama da tsananain hareharen ‘yan bindinduga a yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya.
Discussion about this post