Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai cilla kasar Amurka domin halartar taron majalisar ɗinkin duniya.
A sanarwar da Femi Adesina ya fitar kuma ya saka wa hannu ranar Asabar, shugaba Buhari zai tashi zuwa kasar Amurka ranar Lahadi, kuma zai yi jawabi a wurin taron majalisar ɗinkin duniya, a zauren UN din.
Haka shima mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya tashi zuwa kasar Birtaniya domin halartar Jana’izar marigayiya sarauniyar Ingila, Elizabeth wanda ta rasu a cikin makon jiya.
Mai taimaka wa Osinbajo kan harkokin yaɗa labarai Laolu Akande da shine ya fodda sanarwar ba faɗi ranar da mataimakin shugaban kasan zai dawo Najeriya ba.