Wani jigon APC a Jihar Jigawa, mai suna Isah Gerawa, ya bayyana rashin jin daɗin sa dangane da yadda Gwamna Abubakar Badaru ke danƙara kisan dukkan manyan kwangilolin jihar ga waɗanda ba Musulmi ba.
Wannan zargin da Gerawa ya yi dai ya ce Badaru ya na fifita Kiristoci bisa Musulmai ‘yan asalin Jihar wajen bayar da kwangiloli, duk kuwa da cewa su Kiristocin ba ‘yan jihar ba ne, kuma ba ma a jihar su ke zaune ba.
Ya ce idan aka zaɓi Umar Namadi da ke takarar gwamna ƙarƙashin APC, ba zai yarda ya ci gaba da irin yadda Badaru ke watsar da ‘yan jihar wajen bayar da kwangiloli ya na bai wa waɗanda ba Musulmai ba.
Gerawa ya yi wannan ɓaɓatu ne a lokacin da magoya bayan APC su ka kai masa ziyara a gidan sa.
“Abin takaici ne matuƙa yadda Gwamna ke bai wa waɗanda ba musulmai na kwangiloli. Kuma ba su amfana wa al’ummar jihar.
Jihar Jigawa dai akasarin ta musulmai ne kuma APC ce ke mulkin Jihar.
Gerawa wanda hamshaƙin attajiri ne, kuma ɗan siyasa, ɗan jihar Jigawa ne, mazaunin Kano, kuma shi ne ke da katafaren masana’antar sarrafa man ƙuli da shinkafa ta Gerawa Oil da kuma Gerawa Rice. Ya na ɗaya daga cikin masu tashe a Kano.
“Tsawon shekaru huɗu kenan ban samu ko sisi a Jigawa ba. Amma ina kallo ana danƙara kwangiloli ga waɗanda ba Musulmi ba, kuma ba za su amfana wa jihar komai ba, sai ma cutar da ‘yan jihar. Saboda haka mu na son a daina wannan ɗabi’a. Shi ya sa za mu riƙa faɗin gaskiya a fili.
“Shekara huɗu ko sisi ba a ba ni ba, duk abin da na ke kashewa daga wasu hanyoyi na ke samun kuɗin.
Sai dai kuma bayan ya yi wannan magana, an riƙa watsa wata murya inda Gerawa ya ke godiya ga Badaru, saboda “ya ba ni kwangilar aikin titi ta cikin 2015, kuma cikin 2019 ya kai ni ga Ministan Ayyuka Babatunde Fashola ya ba ni kwangila ta naira biliyan 81.”
Kakakin Gerawa mai suna Muttaqa Namadi ya ce tabbas maganar da Gerawa ya yi, gaskiya ce shi ne ya faɗa.
Discussion about this post